--
Tirkashi: Duba Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano

Tirkashi: Duba Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano


Mazauna wasu unguwanni na fama da korafi a kan sace-sacen garin tuwo da ake masu a wajen nika a birnin Kano - Faruwar wannan al'amari ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika 


Sai dai an danganta wannan lamari da halin da talaka ya tsinci kansa a ciki na matsayin rayuwa da tsadar kayan masarufi A yayinda talakawa ke ci gaba da kukan babu da matsin rayuwa, mazauna wasu unguwanni a birnin Kano, na korafi a kan yadda ake sace masu garin tuwonsu a wajen nika a yan kwanakin nan. 


A lokutan baya da wuya ka ji an ce an sace garin tuwo a wurin nika sai dai a samu yanayin da ake yin musaya bisa kuskure, wato wani ya dauki na wani. An tattaro cewa wannan sabon sauyi da aka samu na sace-sacen garin ya sanya wasu masu injin nika sun fara ba da katin shaida domin rage afkuwar hakan. 


A yanzu idan mutum ya kai nika, sai a bashi katin shaidar cewa ya kai nika wajen. Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da wani rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce an samu karin mutum fiye da miliyan guda da ke fama da karancin abinci a jihar Kano sakamakon annobar korona, 


sashin Hausa na BBC ta ruwaito. Sai dai kuma, mutane da dama na danganta al'amarin da irin matsin rayuwar da jama'a suka samu kansu a ciki saboda tashin gwauron zabi da farashin kayan masarufi ya yi. An dai samu tashin farashin kayayyaki sakamakon karin kudin man fetur da wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta yi. 


Source: Legit.ng 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Tirkashi: Duba Yadda satar garin tuwo ta tilasta ba da katin shaida a wurin nika a Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?