Tirkashi: Dan sanda ya tsere bayan bindige budurwarsa a baki
Wani jami'in dan sanda a jihar Legas ya harbi budurwarsa a bakinta ya mata mugun rauni sannan ya tsere Faifan bidiyon budurwar da ya bazu a dandalin sada zumunta ya nuna ta cikin azaba yayin da mutane suka garzaya da ita asibiti
Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta ce ta gano dan sandan da ya yi harbin kuma za ta kamo shi don bincike Wani dan sanda da har yanzu ba a gano sunansa ba ya tsere bayan ya harbi budurwarsa a bakinta a Salvation Bus Stop da ke Ikeja a Legas. An ruwaito cewa dan sanda ya gudu ya bar budurwarsa a wurin bayan aikata laifin.
Faifan bidiyon lamarin da ke yawo a dandalin sada zumunta ya nuna matarsa tana cikin azaba yayin da wasu mutane suka taimaka suka garzaya da ita asibiti don yi mata magani. A cikin bidiyon ana iya ganin yadda kumatun matar ya fashe saboda harsashin da ya ratsa ta bakin ta.
An kuma nuna lokacin da matar ke zaune a kasa a asibiti tana fama da azaba yayin da ta ke jiran lititoci su zo su duba ta. Da aka tuntube shi, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Muyiwa Adejobi ya ce, "An gano dan sandan, ba rundunar Legas ya ke ba amma an turo shi aiki a jihar Legas."
"Saurayin matar ne; za mu kamo shi. Muna tsamanin sun samu sabani ne hakan ya janyo harbin. An aike da 'yan sanda zuwa asibitin don duba matar kuma su mata tambayoyi idan ta samu sauki."
Source: Legit.ng
0 Response to "Tirkashi: Dan sanda ya tsere bayan bindige budurwarsa a baki "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?