
Tallafin Covid-19: An gane mahaifina ba shine matsalar Najeriya ba - Zahra Buhari
A 'yan kwanakin da suka gabata ne 'yan Najeriya suka gano ma'adanar kayan tallafin COVID-19, kuma suka shiga suka kwashe kayan abincin tas
Hakan ya kawo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani, wanda har wata mai shirya fina-finai, Mansurah Isah ta yi wata wallafa a Instagram - Tace ga dukkan alamu, shugaba Buhari ba matsalar Najeriya bane, tunda ya bayar da kayan abinci, rabawa ne ba a yi ba,
Zarah Buhari ta kara wallafa wannan wallafar ta Mansurah Kwanaki kadan da suka gabata, 'yan Najeriya sun gano ma'adanar da aka killace kayan abincin tallafin COVID-19 wanda CACOVID suka bayar, kuma sun fada gidajen sun kwashesu tas.
Kayan tallafin sun hada da kayan abinci iri-iri wadanda ya kamata a rabawa talakawan Najeriya. 'Yan Najeriya da dama sun yi ta caccakar gwamnatin jihohi a kan rashin raba kayan abinci da ya kamata su yi lokacin da aka shiga tsanani.
Wata mai shirya fina-finai, Mansurah Isah, ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta nuna yadda aka gano kayan tallafin, wanda hakan ke nuna ba shugaban kasa ne matsalar Najeriya ba.
Zarah Buhari-Indimi, wacce diya ce ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta kara wallafa wallafar Mansurah a shafinta na Instagram, da alamu ta yadda da abinda Mansurah Isah ta wallafa.
Source: Legit
0 Response to "Tallafin Covid-19: An gane mahaifina ba shine matsalar Najeriya ba - Zahra Buhari "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?