--
Soyayyah Ruwan zuma: yadda wani dan bautar kasar ya nemi auren kyakyawar budurwarsa bayan ya yi suman karya

Soyayyah Ruwan zuma: yadda wani dan bautar kasar ya nemi auren kyakyawar budurwarsa bayan ya yi suman karya


Wasu masoya biyu da suka kasance yan bautar kasa sun nuna wa duniya ainahin soyayya ta gaskiya - Da yake neman auran yarinyar, matashi mai yiwa kasa hidimar ya yi karyan kamuwa da rashin lafiya mai tsanani, lamarin da ya jefa budurwar tasa cikin rudani 


Yayinda kyakyawar budurwar ta shiga rudani, sai saurayin ya ciro zobe sannan ya nemi ta aure shi A wani lamari da za a iya kira da sabon salon neman aure, wani matashi dan Najeriya ya nemi auran kyakyawar budurwarsa. 


Kasancewar masoyan biyu duk masu yiwa kasa hidima ne wato NYSC, saurayin ya yi suman karya inda yayi kamar ya kamu da ciwon ciki mai tsanani. Mawuyacin halin da yayi karyan shiga ya sa hankalin budurwar nasa tashi inda ta shiga rudani, tana ta ihun nemawa saurayin nata agaji daga mutanen da ke kallonsu. 


Tuni dai bidiyon ya shahara a soshiyal midiya, yayinda wani ya zo da ruwa domin ya yayyafa masa, a take sai saurayin ya fito da zobe daga aljihunsa sannan ya mikawa budurwar. Lamarin ya sanya yar bautar kasar cikin shauki yayinda ta rufe bakinta da hanayyenta cike da farin ciki. Mutane na ta ihun cewa ta amsa masa da Eh. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Soyayyah Ruwan zuma: yadda wani dan bautar kasar ya nemi auren kyakyawar budurwarsa bayan ya yi suman karya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?