
Shugabanni su farka, mulkin kama-karya ne yake fusata matasa - Okorocha
Sanata Rochas Okorocha ya ce mulkin kama-karya ne ya janyo zanga-zangar EndSARS a Najeriya - Tsohon gwamnan kuma jigon jam'iyyar APC ya ce matasa na yin zanga-zangar ne don farkar da shugabanni
Okorocha ya ce yanayin rayuwa mai cike da almubazzaranci da shugabanni suke yi shine ke kara harzukar da matasan Rochas Okorocha, tsohon gwamnan jihar Imo, ya yi bayani dalla-dalla a kan dalilan da ke hassalar da matasa suna tada hankulan jama'a, asarar dukiya da kuma tayar da zaune tsaye da sunan zanga
zangar EndSARS. A ranar Juma'a, 23 ga watan Oktoba, yayin da Sanatan, kuma tsohon gwamnan, wanda yanzu haka shine mai wakiltar mazabar Imo ta yamma, ya yi hira da manema labarai a Abuja, inda yace mulkin kama-karya, zalunci, kunci, bala'i da yunwa ne dalilin da ya tunzuro matasa suka mayar da zanga-zangar EndSARS tashin hankali.
Okorocha ya jajanta wa wadanda suka rasa 'yan uwansu, yaransu da masoyansu sakamakon rikicin. Ya ce yanayin rayuwa cikin wadata da almubazzaranci da shugabanni suke yi shi ke tunzura matasan.
Ya ce ya kamata a yanke kaso 50 zuwa 70 na kudaden da ake shaka wa gwamnoni da ministoci, don suma matasa su samu sassauci. Y
a ce yakamata shugabanni su rage yanayin yadda suke kashe kudi yadda suka ga dama, domin wannan zanga-zangar alama ce da matasan ke nuna musu cewa sun gaji. Ya ce shugabannin kasar nan na nuna son kansu karara wurin tafiyar da mulkinsu, wanda hakan bai dace ba.
Source: Legit
0 Response to "Shugabanni su farka, mulkin kama-karya ne yake fusata matasa - Okorocha "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?