--
Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja

Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja


Zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS ta fara sauya salo a sassan Najeriya da ta samu karbuwa - Rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa ana yawan samun kai hari a kan ma su zanga-zangar adawa da ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS 


Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa atisayen 'murmushin kada' da ta kaddamar bashi da alaka da kowacce zanga-zanga An fito da dakarun soji zuwa kan titunan Abuja domin shawo kan zanga-zangar ENDSARS da ta fara sauya salo. 


Zanga-zangar ENDSARS a Abuja ta fara sauya salo tare da neman rikidewa zuwa rikici sakamakon harin da wasu batagari ke kaiwa ma su zanga-zangar. Batagari a Abuja na kai hari kan ma su zanga-zangar nuna adawa da rundunar SARS da kuma ma su zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS. 


Lamarin, a yawancin lokuta, ya haddasa gumurzu tare da zama sanadiyyar raunata mutane da kuma lalata dukiya. 


Wasu rahotanni sun bayyana cewa wani daga cikin ma su zanga-zanga ya rasa ransa a asibitin da aka kai shi sakamakon mummunan rauni da wasu batagari suka yi masa a Abuja. An ga dakarun soji da safiyar ranar Litinin a sanannen shataletalen AYA, wurin da masu zanga-zanga su ka yi niyyar mamayewa. 


Jaridar The Nation ta rawaito cewa an ga dakarun soji sun saka garkuwa a kan titin domin tabbatar da cewa ma su zanga-zangar basu rufe hanya tare da haddasa cunkuso ba. 


A jiya, Lahadi, ne rundunar soji ta sanar da cewa sabon atisayen 'murmushin kada' da ta kaddamar bashi da wata nasaba da zanga-zangar da matasa ke yi a kan rushe rundunar SARS da zaluncin 'yan sanda. 


A cikin wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta fitar (DHQ), kanal Sagir Musa, kakakin rundunar soji ya ce kuskure ne a bayyana cewa an kaddamar da atisayen ne saboda zanga-zangar ENDSARS da ake yi a sassan kasa. Kanal Sagir ya bayyana cewa rundunar soji ta nuna kwarewar aiki tun bayan barkewar zanga-zangar kusan sati biyu da su ka wuce. 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

Related Posts

0 Response to "Sauya salon zanga-zanga: An sako sojoji zuwa titunan Abuja "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?