
Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Borno (Bidiyo)
Saturday, 17 October 2020
Comment

Sojin sun samu labarin kasancewar yan bindigan a wajen ne daga bakin mutane Rundunar mayakan saman Najeriya (NAF) karkashin atisayen Operation LAFIYA DOLE sun samu nasarar ragargaza wani sansanin yan ta'addan Boko Haram da ISWAP dake yankin tafkin Chadi a Borno.
Jami'an sun samu nasarar yin hakan ne a harin da suka kai ranar Alhamis, 15 ga Oktoba. Hedkwatar tsaro ta bayyana cewa "rundunar sojin sun kashe yan ta'addan ISWAP da dama kuma suka ragargaza sansaninsu dake Tudun Wulgo da Tumbin Gini dake yankin tafkin Chadi dake jihar Borno."
A jawabin da kakakin hedkwatar tsaro ya saki a shafinta na Tuwita, ya ce "an samu nasaran hakan ne a ruwan saman da aka kai jiya 15 ga Oktoba, 2020 karkashin hari mai taken "WUTAR TAFKI,."
Kalli bidiyon harin:
#PressRelease #DHQUpdate
— DEFENCE HQ NIGERIA (@DefenceInfoNG) October 16, 2020
AIR TASK FORCE OF OPERATION LAFIYA DOLE NEUTRALIZES ISWAP TERRORISTS, DESTROYS HIDEOUTS AT TUDUN WULGO, TUMBUN GINI IN BORNO STATE https://t.co/dL0vxSHmag pic.twitter.com/JPrDnUE6JH
A bangare guda, wani faifan bidiyo ya bayyana a kafafen ra'ayi da sada zumunta inda aka yi takaddama tsakanin wasu jami'an sojoji da yan sanda a kan titi.
A cikin bidiyon, ana iya ganin lokacin da wani jami'in Soja yake marin dan sanda kan abinda yake yiwa fasinjojin dake wucewa. Mun ji Sojan yana magana yana dukan dan sandan: "Me yasa kuke amsan kudi a hannunsu, ku mayar musu da kudadensu."
0 Response to "Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Borno (Bidiyo)"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?