--
NCC Ta Samar Wa Nijeriya Kudin Shiga Naira Tiriliyan 2.272 – Umar Dambatta

NCC Ta Samar Wa Nijeriya Kudin Shiga Naira Tiriliyan 2.272 – Umar Dambatta


Shugaban hukumar sadarwaa ta kasa (NCC), Umar Garba Dambatta ya bayyana cewa, bangaren sadarwa ya samar wa kasar nan kudaden shiga mai yawa wanda ya kai tun daga kashi 8.5 a shekarar 2015 zuwa na kashi 14.3 a cikin watan Satumbar wannan shekara, wanda ya kai na naira tiriliyan 2.272. 


Dambata ya bayyana hakan ne lokacin da mambobin kwamitin majalisar wakilai masu kula da bangaren sadarwa, wanda Akeem Adeyemi yake jagoranta suka ziyarci hukumar domin gudanar da aikinsu na kulawa da bangaren sadarwa. 


Haka kuma, shugaban hukumar ya bayyana cewa, an zuba jari a bangaren na naira biliyan 38 a shekarrar 2015, yayin da yanzu akwai hannun jari sama da na naira biliyan 70, inda a yanzu hukuamr da ke iya biyan haraji a asusun tarayya wanda ya kai na naira biliyan 344, a duk shekara.


Ya dai bayyana adadin wadanda suke amfani da sadarwa a Nijeriya sun kai mutane miliyan 205.25, wanda suka karu da kashi 107 a karshen watan Satumbar shekarar 2020. Ya kara da cewa, duk da yawan mutanen Nijeriya ya kai miliyan 200, wasu daga cikin masu amfani da harkokin sadarwa ba sa amfani da yanar gido, yayin da wasu kuma suke yi.


“Lokacin da muka shiga ofis a shekarar 2015, mun gudanar da wasu tsare-tsare a tsakanin shekarar 2015 zuwa shekarar 2020. Wadannan tsare-tsare sun sa an yi matukar samu nasarar bunkasa harkokin sadarwa a Nijeriya. Daga cikin tsare-tsaren akwai yin amfani da wasu abubuwa wadanda za su kara inganta ayyukan sadarwa da kuma bai wa masu amfani da sadarwa kariya.


“A zuwa lokacin da aka gudanar da wannan kididdiga, an samu karuwar kudaden shiga da kashi 8.5 na shekarar 2015 zuwa kashi 14.3 wanda muke da shi a halin yanu. A tsakiyar wannan shekara, an  samu haraji wanda ya kai na kashi 15.5.


 
“Lokacin da muka hade dukkan yawan harajin da muka samu sai muka ga ya ba mu yawan kudade wanda ya kai na naira tiriliyan 2.272, a tsakiyar wannan shekarar ta 2020, tun dagaa shekarar 2015 har zuwa yau.


“Wannan ya nuna cewa, lallai tsarin da ake bi wajen gudanar da harkokin sadarwa suna kara bunkasa yadda ya kamata a cikin kasar nan.


“Yawan hannun jarin da aka zuwa a bangaren sadarwa a shekarar 2015 ya kai na naira biliyan 38, amma a yanzu akwai sama da dala biliyan 70. Tsakanin shekaru biyar da suka gabata, mun saka naira biliyan 344.71 a cikin asusun tarayya na haraji, inda muka saka sama da biliyan 70 a duk shekara.


 
“Muna neman hadin kai kwamitin majalisa wajen cimma burikan da muka saka a gaba a shekarar 2023 na samar wa gwamnatin tarayya kashi 80 cikin kudaden shiga.


“Kamar yadda nake magana da ku a halin yanzu, ana kara samun yawan masu amfani da harkokin sadarwa a Nijeriya da kashi 1.5 a dun sakan,” in ji shi.


Shi ma shugaban kwamitin majalisa da ke kulawa da harkokin sadarwa, Hon. Akeem Adeyemi ya bayyana cewa, ayyukan kulawan da suke a cikin sadarwa dai shi ne, ya tabbatar da hukumar tana gudanar da aiki yadda ya kamata kamar yadda tsarin mulki ta tanada.



A cewarsa, a karkashin tsarin rarraba makaman gwamnati, kowani sashe na gwamnati akwai irin ayyukan da yake gudanarwa na sa ido, domin a kaucewa barnatar da dukiyar gwamnati da kuma yin amfani da karfin iko wajen karya doka da oda.



“Wannan ne ya sa majalisa take da ikon saka ido a cikin ayyukan sauran matakan gwamnati musamman ma a bangaren zantarwa wanda ke kashe kudade domin ‘yan kasa.


 
“Ayyukan saka ido yana taimaka wa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen cimma shirinsa na ceto ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga kangin talauci, wanda ayyukan NCC za ta iya taimakawa sosai domin cimma burin. Kwamitin za ta duba kasafin kudin hukumar yadda ya kamata domin aiwatarwa,” in ji shi.


Source: https://hausa.leadership.ng/ncc-ta-samar-wa-nijeriya-kudin-shiga-naira-tiriliyan-2-272-dambatta/

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "NCC Ta Samar Wa Nijeriya Kudin Shiga Naira Tiriliyan 2.272 – Umar Dambatta"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?