--
Na kama matata ta na cin amanata da magidanci a gadonmu na aure - Tsohon minista Femi Kayode

Na kama matata ta na cin amanata da magidanci a gadonmu na aure - Tsohon minista Femi Kayode


Bayyanar faifan bidiyon tsohon minista Femi Fani Kayode (FFK) ya na zazzagawa tsohuwar matarsa masifa sun haddasa cece-kuce a dandalin sada zumunta - Har yanzu FFK bai saki matarsa ta hudu ba duk da sun dade basa zaune tare sakamakon rikicin 'da ya ki ci, ya ki cinyewa' a tsakaninsu 


Ana yawan zargin FFK tare da sukarsa a kan rashin hakuri da mata Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode, ya magantu a kan wani faifan bidiyo da ke nuna shi ya na zazzagawa matarsa da su ka rabu, Precious Chikwendu, masifa. 


FFK ya garzaya shafinsa na Instagram domin kare kansa a yayin da wasu kafafen yada labarai da ma'abota dandalin sada ke caccakarsa a kan rashin hakuri da mata. A cewar ministan; "SaharaReporters ta wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna ni a matsayin mai cin zarafin matarsa.


"Wannan ba wani abu bane face yada farfaganda da son batamin suna. "Babu wani abu a faifan bidiyon sai kokarin da na ke yi na son karbe wayarta ta hannu domin hanata nadar sabanin da muka samu. 


"Babu inda aka ga na ci zarafinta a faifan bidiyon, hatta fadan da na ke yi saboda na kamata ta na cin amanata da wani mutum mai aure ne. 


"Na kara maimaita cewa ban ci zarafinta ba, ita ce ta ke cin zarafin jama'a, halinta ne cin zarafin jama'a tare da wulalantasu kamar yadda ta ke yi wa 'yan uwana, ma'aikatana, kananan yara da leburorin da ke aiki gidanmu. 


"Za a iya sauraron kalamaina a faifan bidiyon, na fada ma ta cewa kowa zama lafiya ya ke so amma banda ita. Bam taba cin zarafinta ba duk da na kamata da kwarto," a cewar FFK. 



View this post on Instagram

@SaharaReporters posted a video which supposedly depicts me ABUSING my estranged wife.This is nothing but a propaganda video.There was NO physical abuse.I simply took the phone from her to stop her from recording me after catching her in bed with a married man days earlier. I repeat there was NO physical abuse whatsoever and she had been insulting and subjecting everybody, including family members, staff and children, to PHYSICAL and VERBAL abuse the whole day. As usual, it was a nightmare! My words in the video are self explanatory. I urge those thet watched it to listen to those words carefully. I told her that everyone wanted peace except for her and all she did was indulge in scandal after scandal. I have NEVER physically abused my estranged wife.

A post shared by Femi Fani-Kayode (Sadauki) (@real_ffk) on


 Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Na kama matata ta na cin amanata da magidanci a gadonmu na aure - Tsohon minista Femi Kayode"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?