--
Mutum 3 sun tone kabari 10 suka datse kawunan mamata domin tsafi

Mutum 3 sun tone kabari 10 suka datse kawunan mamata domin tsafi


Yansanda sun gurfanar da wasu uku a gaban Kotun Maajistare a Ado-Ekiti bisa zargin hakar Kabari suka tone gawakin 10 da aka binne kuma suka yanke kawunasu bisa dalilan tsafi.

Wadanda aka kama su ne Kola Fatoye mai shekara 40, da Abimbola Fatoyedan shekara 35, da Ahmed Ojo, shekara 56 a Duniya.


Mai gabatar da kara ta yansanda Monica Ikebuilo ta gaya wa Kotu cewa wadanda ake zargi sun aikata laifin ne tun watan Maris zuwa Satumba a garin Prun-Ekiti.


Ikebuilo ta ce gawakin da mutanen suka tone na Philip Akintayo, Moreani Ajayi da wasu mutun takwas ne., kuma sun yi hakan ne bisa dalilan tsafi, kamar yadda ta gaya wa Kotu.


Source:Isyaku.com

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Mutum 3 sun tone kabari 10 suka datse kawunan mamata domin tsafi"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?