
Mutane za su koma sayen 1GB a kan N390 maimakon N1000 a Najeriya
Shugaban hukumar NCC ya ce su na shirin sake rage farashin ‘Data’ - Ma’aikatar sadarwa ta ci burin yin wannan aiki nan da shekarar 2025
Duk da haka Najeriya ta na cikin kasashe masu arahar ‘Data’ a Afrika Shugaban hukumar NCC mai kula da sadarwa, Umar Danbatta, ya ce ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta na shirin rage farashin ‘data’.
Data shi ne abin da ake saida wa masu hawa shafukan yanar gizo da manhajojin sada zumunta. Hukumar NCC ta bayyana haka ne a lokacin da shugabanta ya yi magana da ‘yan jarida a Kano. NCC ta ce su na kokarin rage kusan 60% na kudin ‘data’.
Farfesa Umar Danbatta ya ce za a koma saida kowane 1GB a kan N390, a maimakon N1, 000. Farfesan ya ce wannan ya na cikin dogon burin NCC. A wannan shiri da NCC ta ke yi na 2020 – 2025, na’urorin 4G za su karade Najeriya, sannan za ayi kokarin ganin karfin hawa yanar gizo ya shiga ko ina.
Farfesan ya na mai cewa, an ba ma’aikatar sadarwa nauyin ganin an bullo da dabaru ta yadda kamfanonin MNO za su rage kudin da su ke saida ‘data’. Danbatta ya ce ana so a rage tsadan ‘data’ daga N1, 000 da aka saba saye zuwa N390. Wannan duk da kokarin da aka yi na rage farashin a kwanakin baya.
“Hakika farashi ya ragu zuwa kowane 1GB a kan N1, 000, amma gwamnati ta ce mu yi harin N390 nan da shekaru uku zuwa shekaru biyar.” Inji Danbatta. Kafin a iya samun wannan rangwame, sai gwamnati ta gina abubuwan da ake bukata.
A halin yanzu kasashen Afrika kadan su ka fi Najeriya arahar ‘data’. Kwanakin baya Ministan sadarwa ta tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami ya bada labarin yadda ake tara masa takardun neman aiki a duk jihar da ya je. Dr. Isa Pantami ya ce daga ya kai ziyara jihohi sai a rika mika masu takardun masu neman aiki.
Source: Legit.ng
0 Response to "Mutane za su koma sayen 1GB a kan N390 maimakon N1000 a Najeriya "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?