
Mun ɗaura ɗamarar yaƙi da aƙidun addinin Islama – Faransa
Friday, 30 October 2020
Comment
Ministan cikin gida na Faransa Gerald Darmanin ya ce Faransa na yaki da akidun Islama, bayan kashe wasu mutane uku a wata coci da ke kudancin birnin Nice.
Ya yi gargadin kara samun irin wadannan hare-hare, sai dai ya jaddada cewa Faransa ba ta yaki da wani addini.
Jagoran 'yan adawar kasar Marine Le Pen ta yi kira ga gwamnati ta bijiro da dokokin gaggawa don tasa keyar masu kaifin kishin Islama zuwa kasashensu na ainihi.
Shugaba Emmanuel Macron zai sake gudanar da wani taro na majalisar tsaro don tattaunawa game da harin Nice da kullen korona, wanda ya fara aiki da tsakar dare.
Wanda ake zargi da kisan na birnin Nice na cikin mawuyacin hali a asibiti bayan 'yan sanda sun harbe shi.
Source: Bbc Hausa
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Mun ɗaura ɗamarar yaƙi da aƙidun addinin Islama – Faransa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?