Mu leka kotu: Alkali ya warware auren shekaru 35 saboda mijin ya gaza biyan sadaki
Wata kotun zamantakewa a jihar Ekiti, ta warware auren shekaru 35, saboda mijin ya gaza biyan sadaki - Babbar alkalin kotun, Yemisi Ojo, ta warware auren, tana mai cewa bangarorin biyu na zaman auren ne kawai tamkar dadiro ba wai a shari'an ce ba
Ta shawarci macen da ta karfafa guiwar 'yayansu 5 wajen ziyartar mahaifinsu don ci gaban zumunci a tsakanin su Wata kotun zamantakewa a jihar Ekiti a ranar Laraba ta warware wani auren shekaru 32 tsakanin Oladipo Ogunleye da Adeola Falade saboda gaza biyan sadaki Babbar alkalin kotun,
Yemisi Ojo, ta warware auren, tana mai cewa hujjoji sun bayyana, na cewar ana zaman auren ne kawai tamkar dadiro ba wai a shari'an ce ba. Ta bai wa bangarorin biyu umurni da kowannensu ya kama gabanshi kasancewar yanzu babu aure a tsakanin su.
"Ina shawartar mai karar da ya karfafa alakarsa da 'yayansa biyar. Ina shawarar ita macen da ta karfafa guiwar 'yayan wajen ziyartar mahaifinsu don ci gaban zumunci a tsakanin su.
"Kotu ta bayar da umurni ga namijin da ya rinka biyan kudin makarantar yaran. Ina shawartar bangarorin biyu su yi zaman lafiya," a cewar ta. Haka zalika, ta gargadi bangarorin biyu da cewar duk wanda ya karya dokokin da kotun ta shar'anta, zai fuskanci hukuncin shari'a.
Tun farko, mai karar, Ogunleye mai shekaru 61, bakanike, a hujjojinsa ya bayyana cewa babu aure tsakaninsa da matar, suna zaman dadiro ne kawai, har suka haifi yara biyar. Ogunleye ya ce a tsawon zamansa da matar, ya dauki dukkanin nauyin ta da na yaran, amma tunda matar ta tsallake ta bar yaran, ya daina kula da su.
Mr Ogunleye, ya roki kotun da ta kawo karshen wannan alaka da ke tsakaninsu, kuma a lokaci daya, yana rokon a bar masa yaran biyar ya ci gaba da kula da su. Sai dai Miss Falade mai shekaru 48, ma'aikaciyar gwamnati, ta musanya wannan zargi da Ogunleye ya yi mata. "Mijina na dukana kuma yana korata. Kuma ya jima yana yi mun barazanar zai kore ni daga gidan kwata kwata," a cewar ta.
Source: Legit.ng
0 Response to "Mu leka kotu: Alkali ya warware auren shekaru 35 saboda mijin ya gaza biyan sadaki "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?