Ministan Buhari da babban basarake sun sha da kyar hannun 'yan daba
Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya bayyana yadda wasu 'yan ta'adda suka kai hari fadar sarkin Ogbomoso suna tsaka da wani taro - Yace 'yan ta'addan ba dalibai ko matasa bane, 'yan iskan gari ne da ke neman damar tadawa mutane hankula, saidai da taimakon 'yan sanda komai ya daidaita
Duk da ministan, sarkin da sauran manyan mutane da suka halarci taron na cikin koshin lafiya, 'yan ta'addan sun farfasa kofofi, tagogi, kujeru, da sauran abubuwa a fadar Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, yace wasu 'yan ta'adda sun kaiwa fadar babban basarake dake Ogbomoso hari.
Yace sun katse musu wani taro da suke yi tare da basaraken, Oba Oladunni Oyewumi a ranar Lahadi. Jaridar The PUNCH ta tattaro bayanan yadda jami'an tsaro suka samu nasarar ceto ministan, basaraken da kuma sauran manyan mutane da suka halarci taron.
Amma kuma wakilinmu ya kasa tabbatar da ko 'yan ta'addan sun kaiwa ministan hari ne ko kuma wani daga cikin manyan mutanen. Ministan ya sanar da yadda 'yan bindigan suka lalata abubuwa da dama a fadar. Ya tabbatar da aukuwar lamarin ne a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda ya wallafa, "
Wasu 'yan ta'addan Ogbomoso sun kai wa fadar Sarkin Ogbomoso hari, inda suka ritsa mu muna tsaka da taro. "Sun fara rusa kofofi da tagogin kwalabe da duwatsu muna tsaka da taron. 'Yan sanda sun samu nasarar ceto na, sarkin da kuma manyan mutanen da suka halarci taron."
Ya kara da cewa, "Ba dalibai bane ko kuma matasa, 'yan iskan gari ne kawai da ke neman damar da za su tada hankulan jama'a. Sai dai saukin da aka samu shi ne, basu yi nasarar taba sarki, shugabannin Parapo, da kuma manyan mutanen da suka halarci taron ba."
Ministan yayi mamakin dalilin da zai sa su kai hari fadar sarkin, duk da Sarkin yana tabbatar da zaman lafiya a garin. Dare ya kara da cewa, "Matasan Ogbomoso suna da bin doka. Amma wadannan 'yan ta'addan sun rinjaye su.
Jami'an tsaro masu tarin yawa sun taho tun daga Ibadan, wasu kuma daga Ilorin, suna kula da fadar, kuma suna iyakar kokarinsu wurin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin jama'ar." Jiya da yau, Sarkin Ogbomoso da kansa ya fito ya bada hakuri akan tada hankulan jama'a da 'yan ta'addan suka yi.
Source: Legit
0 Response to "Ministan Buhari da babban basarake sun sha da kyar hannun 'yan daba "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?