--
Mawaki Saleem smart ya kafa tarihi da wakarsa ta zomu sasanta a kannywood

Mawaki Saleem smart ya kafa tarihi da wakarsa ta zomu sasanta a kannywood



Daga El-farouq jakada

Wani matashin mawaki Mai tasowa Mai suna Salim smart ya kafa tarihi a masana'antar shirya fina-finai ta kannywood Dake arewacin najeriya.
Matashin Ana kyautata zaton zai Zama mawaki na farko Mai irin basirarsa da Kuma baiwarsa, duk da cewa akwai matasa irinsa hakan Bai Hana yayi musu fintinkau a fannin ba.

Salim ya kafa wannnan tarihin da wakarsa Mai suna "zomu sasanta " Wanda aka cire wakar a matsayin ta saurare cikin kankanin lokaci sama da mutum dubu sukayi 'yar guntuwar vidiyonta suna Dora a shafukan su na sada zumunta mussaman tiktok, da Instagram, WhatsApp da saurasu.

Wanda Bidiyon Wakar jarumi Kb International da Aisha Izzar So da Ruky Emm suka hau kai.
Cikin Wadanda sukayi hada matar shahararren mawakin nan ado isah (gwanja) bayan irinsu, jaruma momy gombe, zpreety, hafsat Idris (Barauniya) da Aisha najamu (izzar so) ga Zahra diamond da Amal Umar dadai sauran maza da 'yan mata bila adadin.

Salim ya bayyana hakan yana daga cikin nasarorin dayake samu Bai rasa nasaba da addu'ar iyaye, Domin matukar kabi za'a bika fadar shugaban halitta saw.

Sannan ya yiwa masoyanshi albishir da wasu zafafan wakokin wanda sukafi wannnan kamar sumin tabine . Inji Salim din.

0 Response to "Mawaki Saleem smart ya kafa tarihi da wakarsa ta zomu sasanta a kannywood"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?