Matar aure ta yi wa diyar miji mugun duka, ta sheka lahira
Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa sun damke wata matar aure mai suna Aishatu Umaru - Ana zargin matar da laifin kashe diyar mijinta wacce take riko a hannuta da mugun duka
Matar ta musanta laifinta, inda tace mijinta baya basu abinci kuma hakan yasa yarinyar ke fama da ciwo 'Yan sandan jihar Adamawa sun damke wata matar aure da ake zargi da yi wa diyar mijinta dukan da yayi ajalinta.
Aishatu Umaru ta shiga hannun hukuma a ranar Alhamis bayan makwabta sun kai wa 'yan sanda koken zarginta da suke da kashe diyar mijinta mai suna Walida wacce take rikewa.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Suleiman Nguroje wanda ya zanta da manema labarai a Yola, ya tabbatar da kamen Aisha Umaru daga kauyen Kugama da ke karamar hukumar Mayobelwa ta jihar a kan laifin horo da yunwa da kuma kashe yarinyar.
Ya ce wacce ake zargin a halin yanzu ana tuhumarta a sashin laifuka na musamman kuma za a mika ta gaban kotu.
Amma kuma ko da aka zanta da Aisha, ta musanta kashe Walida inda tace yarinyar tuntuni bata da lafiya amma mijinta ya hana kudin kai ta asibiti. "Ban kasheta ba. Abinda ya faru shine, Walida ta saba zuwa makwabta. Sai na tura daya daga cikin yarana domin kiranta. Tana shigowa na dungure mata kai a matsayin fada, a take kuwa ta fadi.
"Sanin cewa bata da lafiya, sai na gaggauta zuwa gidan dan uwana amma sai na tarar baya nan. "A lokacin da na dawo gida, na samu daya daga cikin makwabtana wacce tace min yarinyar ta rasu. Mijina ne ya janyo haka kuma bayan kama shi da aka yi an sakesa," ta bayyana.
Source: Legit
0 Response to "Matar aure ta yi wa diyar miji mugun duka, ta sheka lahira "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?