
Mataimakin gwamnan Sokoto ya kare kansa game da fitar da N718m don ginin titi zuwa fadar mahaifinsa
Mataimakin gwamnan Sokoto Alhaji Munnir ya yi karin haske game da ginin tagwayen titi da ake yi zuwa fadar mahaifinsa, Sarkin Yamman Kware, Muhammad Dan'iya
Mataimakin gwamnan ya ce gwamnatin jihar da ta gabata ne ta bada aikin ginin titin tun kafin a nada mahaifinsa hakimi
Ya ce aikin na cikin kwangilar ginin titi mai tsawon kilimita 5 da gwamnatin ta bada a kananan hukumomi 23 na jihar
Mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Munnir Dan'iya ya kare kansa game da aikin ginin titi mai tsawon kilomita 1.530 da ake gina wa zuwa fadar sarkin Yamman Kware, Alhaji Muhammad Dan'iya.
Alhaji Muhammadu Dan'iya, wanda shine mahaifin mataimakin gwamnan yana daya daga cikin sabbin hakiman da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya nada kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Rahotanni sun ce ma'aikatar kananan hukumomi da ayyukan cigaba wadda mataimakin gwamnan ke shugabanta ce ta bada kwangilan ginin titin.
Amma kakakin mataimakin gwamnan, Aminu Abdullahi Abubakar ya yi bayanin cewa an bada kwangilar ginin titin tun kafin a nada mahafin mataimakin gwamnan a matsayin hakimi.
Ya ce aikin na cikin kwangilar gina titi mai tsawon kilomita biyar cikin kananan hukumomi 23 da gwamnatin jihar da ta gabata ta bayar saboda haka ba son kai bane yasa aka kirkiri aikin.
Source: Legit.ng
0 Response to "Mataimakin gwamnan Sokoto ya kare kansa game da fitar da N718m don ginin titi zuwa fadar mahaifinsa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?