--
Masu ƙananan sana'oi a Najeriya na dab da samun tallafin gwamnatin Buhari

Masu ƙananan sana'oi a Najeriya na dab da samun tallafin gwamnatin Buhari


Hukumar bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana''o'i a Nijeriya wato SMEDAN, ta ce tana sa rai masu ƙananan sana'o'i fiye da dubu talatin ne za su ci gajiyar shirin gwamnatin tarayya na tallafin bunƙasa jari sakamakon cutar korona.


Hukumar ta ce tuni ta buɗe ofisoshi a wasu jihohi don sauƙaƙa wa masu sana'o'in damar yin rijista don cin gajiyar shirin.


Shirin wanda hukumar ta bullo da shi ta ce wani bangare ne na tallafawa masu karamin karfi domin a rage wa al'umma radadin talaucin da annobar korona ta haddasa.


Hukumar ta ce masu kananan sana'oi a jihohi goma sha daya da suka hada da Kaduna da Kano ne zasu fara cin gajiyar wannan shiri a kashin farko da aka yiwa rijista.


Dakta Dikko Umaru Radda, shi ne shugaban hukumar ta SMEDAN a Najeriya, ya bayyana wa BBC sharuddan da wadanda zasu ci gajiyar shirin zasu cika.


Daga sharuddan akwai cewa dole ne mutum ya kasance dan Najeriya sannan sana'ar da yake yakasance a Najeriyar yake yinta.


Idan kamfanine dole ya kasance yana da rijista da CAC, idan kuma mutum ne mai sana'ar dole ya zamana yana da asusun ajiya na banki da kuma lambar BVN inji shi.


Dakta Dikko Umaru Radda, ya ce wannan tallafi da za a bayar ba bashi bane kyauta ne, gwamnati ce zata bayar saboda ta taimaka wa mutane.


Daga cikin wadanda zasu ci gajiyar wannan shiri har da masu lalurar nakasa wadanda ke yin kananan sana'oi.


Kazalika kungiyoyin mata ma na daga cikin wadanda zasu ci gajiyar wannan tallafi.


To sai dai kuma wasu daga cikin kungiyoyin matan sun koka da cewa yawancin masu kananan sana'oi a cikinsu basu iya amfani da intanet ba.


Hajiya Falmata Abacha, ta kungiyar 'IDLE WOMEN SUPPORT AND EMPOWERMENT' a jihar Kaduna, ta shaida wa BBC cewa, rashin iya amfani da intanet da wasu matan masu kananan sana'oi basu iya ba, anan matsalar take,


To sai dai kuma shugaban hukumar ta SMEDAN, ya ce akwai matakai da suka bullo da su domin magance irin wannan matsala.


Ya ce, "Mun bude ofisoshi a kowacce jiha wadanda ake cewa Help Center, inda duk mai wata matsala musamman ta rashin iya amfani da intanet zai je wajen ayi masa rijista".


Sannan mun yi hadin gwiwa da jihohi inda zasu taimaka su sanya mutane suje kauyuka su basu intanet su basu data domin suje suyi wa mutane rijista saboda kada a bar su a baya in ji Dakta Dikko Umaru Radda.


Source: bbchausa


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Masu ƙananan sana'oi a Najeriya na dab da samun tallafin gwamnatin Buhari"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?