--
Labari da dumi-dumi: IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya

Labari da dumi-dumi: IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya


Shugaban 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da soke rundunar SARS a jihohi 36 na kasar da Abuja - An soke rundunar biyo bayan zanga-zanga da al'umma suka rika yi a tituna da dandalin sada zumunta a kasar 


Rundunar 'yan sandan ta ce za a sauya wa 'yan sandan da ke tsohuwar rundunar ta SARS wuraren aiki nan take Sufeta Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da soke runduna ta musamman mai yaki da fashi da maki wato SARS. 


Ya ce za a tura jami'an da ke tsohuwar rundunar ta SARS zuwa wasu rundunonin na musamman na 'yan sandan. Wannan na dauke ne cikin wata jawabi da ya yi kai tsaye a ranar Lahadi 11 ga watan Oktoban 2020. 


Sanarwar na zuwa ne bayan al'umma sun shafe kwanaki suna zanga-zanga a tituna da kuma dandalin sada zumunta na neman a soke rundunar a kasar baki daya don kisa da cin zarafin al'ummma da suke yi. 


Yayin jawabin, IGP ya ce, "An soke Rundunar tarayya ta musamman masu yaki da fashi da makami da aka fi sani da SARS a dukkan rundunonin 'yan sanda da ke jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja."


 


 Bayan jawabin, kakakin rundunar 'yan sanda na kasa DCP Frank Mba ya fitar da wata sanarwa mai taken, 'IGP ya soke rundunar ta musamman mai yaki da fashi da aka fi sani da (SARS)', wani sashi na cikin sanarwar ya ce: 


"Bisa la'akari da kiraye-kirayen da 'yan Najeriya suka yi, za a tura jami'an tsohuwar rundunar ta SARS da aka rushe zuwa wasu sassa karkashin rundunar 'yan sandan nan take.


"IGP din ya ce ta rundunar ta san cewa akwai bukatar ayi yaki da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka da ke karuwa a kasar da a baya rundunar ta SARS ke yi." 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Labari da dumi-dumi: IGP ya soke rundunar SARS a Najeriya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?