
Kwankwaso ya bude gidan rediyo a Kano, ya nada Maude Gwadabe shugaba
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano ya bude gidan rediyo a Kano - An bude gidan rediyon mai suna Nasara bayan amincewar NBC da aka samu
Baya ga haka, Kwankwaso ya nada Dr. Maude Gwadabe a matsayin shugaban gidan rediyon na farko Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban kungiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso, ya kafa gidan rediyo a jihar Kano kuma ya nada tsohon dan jaridar BBC, Maude Gwadabe a matsayin manajan farko.
Gidan rediyon mai suna Nasara Rediyo, ya samun amincewar hukumar yada labarai ta kasa NBC, da su fara watsa labarai a kan 98.5 FM, Daily Nigerian ta wallafa. A wata takarda da sakataren kwamitin gidan rediyon, Sanusi Dawakin-Tofa ya ce: "An kafa gidan rediyon Nasara ne domin habaka da kare al'umma.
"Akwai jin dadi idan aka samu zakakuran ma'aikata da za su ja ragamar gidan rediyon. Babu shakka Dr. Maude kwararre ne a fannin yada labarai a karni na 21.
Ina taya shi murna tare da sauran ma'aikatan." Dawakin-Tofa ya yi kira ga sauran gidajen rediyon da ke garin Kano da su yi gasa mai kyau tare da kiyaye dukkan dokokin hukumar yada labarai.
Source: Legit
0 Response to "Kwankwaso ya bude gidan rediyo a Kano, ya nada Maude Gwadabe shugaba "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?