
Kwamishina ya zubda hawaye bayan ganin 'satar' da 'yan daba suka yi a Kogi (Kalli Bidiyo)
Lalata cibiyar lafiya ta miliyoyin Naira a kogi ya haifar da damuwa kwarai da gaske - Kwamishinan lafiyar Kogi, Audu, ya fashe da kuka bayan ganin irin barnar da akayi wa kayayyakin aikin lafiyar
Audu ya ce za a kashe makuden kuɗaɗe kafin sake dawo da wajen yadda yake Kwamishinan lafiya a Jihar Kogi, Saka Audu, ya fashe da kuka ranar Laraba, 28 ga watan Oktoba lokacin da yake duba irin barnar da masu fasawa da ƙona dukiyar al'umma suka yi a wata cibiyar lafiya a Jihar da ke Arewa ta Tsakiya.
Gidan talabijin na channels ya ruwaito cewa Audu ya bayyanawa manema labarai cewa kayayyakin miliyoyin naira masu barnar suka lalata.
Audu ya ce daga cikin abubuwan da aka lalata akwai na'urar 'Magnetic Resonance Imaging machine' (MRI) da 'Computer Mammography Machine' da kuma 'Digital Radiography.'
Yace: "Kayayyakin biliyoyin naira duk an sace su. Wanda baza a iya dauka ba kamar su na'urar sanyaya dakin rugakafi, inda muke adana alluran rigakafi, an kuma lalata bangarorin (MRI) da (CT) yadda baza su gyaru ba.
"Wasu kayan kuma an dauke su daga ma'ajiya zuwa daji na kusa kuma an lalata su." Kwamishinan lafiyar Jihar kogi ya kasa rike hawayensa akan irin barnar da akayi wa kayan aikin lafiyar.
A wani bidiyo da gidan talabijin na Channels ya wallafa an nuno kwamishinan yana goge hawaye da bayan hannun sa kuma ya na ƙokarin sa don dakatar da hawayen.
Kogi Health Commissioner Breaks Down In Tears As Medical Store Is Looted and Expensive Medical Equipment Are Vandalised pic.twitter.com/4vSRdmGiZz
— Channels Television (@channelstv) October 29, 2020
Source: Legit.ng
0 Response to "Kwamishina ya zubda hawaye bayan ganin 'satar' da 'yan daba suka yi a Kogi (Kalli Bidiyo)"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?