
Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC
Hukumar NAFDAC reshen jihar Kaduna ta bada muhimmiyar sanarwa ga wadanda suka kwashe abinci - Kwamishinan yada labarai na jihar, ya tabbatar da cewa kayan abincin da magungunan suna dauke da guba
An yi kira ga jama'ar jihar da su sanar da hukumomi wadanda suka kwashe kayan da kuma inda aka adana su Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna (NAFDAC) ta bada sanar da gwamnatin jihar Kaduna cewa kayayayyakin da aka kwashe daga ma'adanarta a yankin Narayi sun hada da magunguna masu tarin hatsari.
"Duk wadanda suka sha wadannan maguungunan suna da yuwuwar kamuwa da manyan cutuka ko kuma mutuwa," kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
"Hukumar kamfanin abincin da aka kwashe musu kaya a ma'adanarsu da ke Kakuri sun tabbatar da cewa sun zuba wa masarar magunguna wanda hakan yasa ba zai yuw a ci ba,"
"A don haka ake shawartar mazauna jihar Kaduna da su kiyaye da abinci ko maganin da za su siya da kuma inda za su siya saboda hatsarinsu. "Gwamnatin jihar Kaduna tana kira ga jama'a da su bayyana wadanda suka kwashe abincin da kuma inda suka boyesu domin gujewa hatsari," kwamishinan yace.
Source: Legit
0 Response to "Ku guji cin abinci da magungunan da aka sata a Kaduna, suna dauke da guba - NAFDAC "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?