--
Kowa yaci ya amayar: Ƴan sanda sun cafke mutane 238 da laifin satar kayan tallafi a Adamawa

Kowa yaci ya amayar: Ƴan sanda sun cafke mutane 238 da laifin satar kayan tallafi a Adamawa


Yan sanda a Jihar Adamawa sun cafke mutum 238 bisa zargin satar kaya a rumbunan ajiyar gwamnati da na jama’a - An kuma yi nasarar kwato wasu kayayyaki daga hannun bata garin da suka sace su a yayin zanga-zangar EndSARS 


Rikici ya fara a jihar ne ranar Lahadi, bayan dandazon matasa sun mamaye dakunan ajiyan gwamnatin jihar a Yola, suka kwashe abincin tallafin korona da aka ba jihar Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kama mutum 184 kan laifin sata a yayin zanga-zangar EndSars sannan ta kama wasu 54 da laifin take dokar kulle da aka saka a jihar. 


Rundunar ta kuma yi nasarar kwato wasu kayayyaki da bata garin suka sata wadanda suka hada da taraktoci 35, adaidaita sahu 12, motoci tara, buhuhunan taki 742, buhuhunan masara 18, kujerun roba 95, inifam din kwastam takwas da sauransu. 


Bata gari da suka fake da zanga-zangar EndSARS suna ta sace-sace a fadin kasar, sun daukaka hare-harensu a ranakun Lahadi da Litinin. Sun yi ta afkawa rumbunan gwamnati da na daidaikun mutane suna ta kwasan duk abunda suka gani. 


An ci gaba da sace-sacen ko bayan da Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya kaddamar da dokar kulle na sa’o’i 24 a ranar Lahadi, jariar The Nation ta ruwaito. Kwamishinan yan sandan jihar Adamawa, CP Olugbenga Adeyanju,wanda ya gabatar da masu laifin da kayayyakin a aka samo ga manema labarai a ranar Laraba, 



ya nuna rashin jin dadi da ganin cewa sace-sacen EndSARS ya gudana a Adamawa. “Bamu taba samun korafe-korafe a kan SARS ba a jihar nan; matsalar da muke da ita kawai sune matasan Shila wandda muka magance,” 


in ji CP din, inda ya kara da cewar bai ga dalilin a yasa jihar ta fuskanci wannan mummunan al’amari ba a alilin EndSARS. Ya kara da cewa, mutanen da suka yi satan da sunan zanga-zangar EndSARS sun kasance miyagu da ke amfani da damar rikicin EndSARS. 


“Muna magana ne a kan bata gari ne; kawai shine magana saboda idan kuna neman tallafi ne kamar yadda masu zanga-zangar EndSARS ke yi, ba wai za ku je hukumar FRSC bane ko hukumar agaji ta Red Cross, 


ko UNICEF ko rumbunan mutane masu zamna kansu ba omin ba a ajiye tallafin korana a irin wadannan wurare,” in ji. Ya ce ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun fara sintirin hadin gwiwa don tabbatar da aminci da dakile zauna-gari-banza daga kai wa dukiyoyin jama’a farmaki a jihar. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Kowa yaci ya amayar: Ƴan sanda sun cafke mutane 238 da laifin satar kayan tallafi a Adamawa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?