
Kotu ta dakatar da KAROTA daga kama baburan adaidaita sahu marasa hatimi A Kano
Hukumar KAROTA ta saka dokar wajibcin mallakar wata takardar hatimi da direbobin adaidaita sahu za su lika a baburansu
Kungiyar direbobin baburan adaidaita ta nuna rashin amincewa da wannan sabuwar doka
Yanzu haka wata babbar kotun jihar Kano ta dakatar da hukumar KAROTA daga muzgunawa direbobin adaidaita sahu ko kuma kama baburansu saboda rashin lika hatimin
Wata babbar kotun jihar Kano ta dakatar da hukumar KAROTA daga yin amfani da jami'anta domin muzgunawa direbobin adaidaita sahu ko kuma kama baburansu saboda rashin lika hatimi(sitika).
Kotun ta dakatar da hukumar KAROTA ne har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci a kan karar da aka shigar a gabanta.
Alkalin kotun, Jastis Jamilu Shehu Sulaiman, ya ce kotunsa ta dauki wannan mataki ne domin sauraron karar da Abdullahi Yahaya Mai-Sango ya shigar.
Lauyan Mai-Sango, Barista Abba Hikima, ne ya nemi kotun ta dakatar da hukumar KAROTA har sai bayan an kammala sauraron karar da su ka shigar.
Jaridar Solacebase da ke Kano ta rawaito cewa Mai-Sango ya shigar da kara amadadin direbobin baburan adaidaita sahu da ke Kano.
A cikin karar da ya shigar da KAROTA da shugabanta, Baffa Babba Danagundi, Mai-Sango ya bukaci kotu ta hana a tilastawa direbobin adaidaita sahu sayen hatimi a kan N8000 tare da cin tarar duk wanda bai siya ba.
Jastis Suleiman ya bayar da umarnin dakatar da KAROTA ne yayin zaman kotunsa na yau, Juma'a, 02 ga watan Oktoba.
Kazalika, ya daga zaman cigaba da sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Oktoba.
Source: Legit.ng
0 Response to "Kotu ta dakatar da KAROTA daga kama baburan adaidaita sahu marasa hatimi A Kano"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?