
Karon farko: Hadimin Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi saboda sukar Buhari
Salihu Tanko Yakasai, hadimin Gwamna Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi - Ganduje dai ya dakatar da hadimin nasa ne saboda sukar shugaba Buhari
Yakasai ya mika godiya ga abokan arziki da suka kira shi don yi masa jaje Hadimin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, wanda ya dakatar, Salihu Tanko Yakasai, ya yi martani a karon farko bayan dakatar da shi.
Ganduje dai ya dakatar da Yakasai ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Oktoba sakamakon sukar Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi kan rundunar tsaron SARS. Yakasai ya mika godiya ga masoya a kan irin kaunar da suka nuna masa bayan labarin dakatarwar nasa ya billo.
Tsohon hadimin na Ganduje a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter ya ce ya ji dadin kulawar da suka nuna masa har cikin zuiyarsa.
“Ina mika godiya ta ga dukkanin mutanen da su ka goya mani baya a jiya, musamman wadanda su ka kira, ko su ka aika mani sakonni ta kafofi dabam-dabam." “Abin ya yi mani yawa sosai, na yi kokarin mayarwa da kowa martani amma na kasa aikata hakan. Nagode sosai har cikin zuciyata.”
I want to sincerely extend my heartfelt appreciation to all those that supported me yday, particularly those that called, or sent messages through several platforms, & those on the TL. I was overwhelmed & I tried to reply to all but couldn't. Thank you from the bottom of my heart
— Peacock (@dawisu) October 12, 2020
A wani labarin, Korarren kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa na jihar Kano, Mu'azu Magaji yayi magana akan dakatar da Tanko Yakasai, mai bada shawara na Musamman akan harkokin yada labarai ga Gwamna Ganduje.
Magaji ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda yace an dakatar da Yakasai. Kamar yadda ya wallafa a shafinsa ranar Lahadi, "Gaskiya ban ji dadin dakatar da Salihu Tanko Yakasai da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi ba.
Salihu amintacce ne ga Gwamna Ganduje.. Ban ji dadin fitarsa ba. Allah ya zaba masa mafi alkhairi!"
Source: Legit
0 Response to "Karon farko: Hadimin Ganduje ya magantu bayan dakatar da shi saboda sukar Buhari "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?