--
Kano: Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna

Kano: Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna

Jami'an hukumar Hisbah ta jihar Kano sun cafke matasa masu askin banza a jihar - Sun tirsasa su a kan tituna inda suka dinga aske musu gashin kansu 


Sun kara da damke masu adaidaita sahu da ke saka hotunan mawaka da jarumai Jami'an hukumar Hisbah a jihar Kano sun tirsasa matasa inda suka dinga aske musu gashin kansu sakamakon askin da suka yi ba na Musulunci ba. 


Sau da yawa jami'an hukumar Hisbah suna damke matasa a jihar Kano a kan laifin saka kaya ba yadda ya dace ba. Su kan tsare masu adaidaita sahu da ke ado da hotunan mawaka ko jaruman fina-finai. Lamarin nan da ya faru ya janyo cece-kuce daga kafafen sada zumuntar zamani. 







A wani labari na daban, wata kotun rundunar soji da ke zama a Maiduguri jihar Borno a ranar Laraba, ta kori wani soja daga aiki tare da yanke masa hukuncin zaman shekaru 5 a gidan yari. Sojan mai suna kofur, Aliyu Yakubu an kama shi da laifin yin fyade a ranar 13 ga watan Yulin 2020 kuma an gurfanar da shi a gaban kotun sojin. 


Kamar yadda soja mai gabatar da kara ya sanar, Yakubu ya ja yarinya mai shekaru 13 zuwa wani kango a ranar 1 ga watan Yulin 2018 a Bama inda ya ci zarafinta kafin ya yi mata fyade. Yarinyar ta sanar da kotun cewa, sojan yayi mata fyade ne yayin da ta bar gidan kanwar mahaifiyarta za ta tafi gidansu. 


"Ya tambayeni inda zani kuma na sanar masa, daga nan ya ja hannuna yace in bi shi,"lauya Aminu Mairuwa, mai mukamin Kaftin ya sanar kamar yadda yarinyar tace. "Ya ja ni zuwa wani kango ta bayan tsohuwar gidan yari sannan ya rufe min baki saboda ina ihu. “Ya fito da wuka tare da yin barazanar kasheni. 


Bayan ya yi min tsirara sai ya kasa shigata. Daga nan ya tambayeni ko an taba saduwa da ni, amma nace a'a. A take ya shigeni ta karfi. "Bayan kammala fyaden, ya yi amfani da bulo wurin fasa min kai kuma ya bar ni ban san halin da nake ciki ba," cewar Mairuwa. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Kano: Hotunan jami'an Hisbah suna yi wa matasa aski a tituna "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?