Kamar Ganduje, Gwamna El-Rufai zai yi wa masarautar Zazzau garambawul
Akwai yiwuwar gwamnatin jihar Kaduna za ta rarraba masarautar Zazzau domin nada wasu sabbin sarakuna - Hakan na zuwa ne bayan Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya sanar da cewa gwamnatinsa na aiki kan wasu kudurori da za ta bawa majalisa don inganta mulki a jihar
Wasu hasashe sun nuna cewa za a raba masarautar ta Zazzau ne zuwa gida uku - Masarautar Kaduna, Zazzau da Kudan kowanne da sarki Gwamnatin Jihar Kaduna tana aiki kan wani kudirin doka da za ta yi garambawul ga yadda tsarin sarauta ya ke a jihar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kudirin dokar na zuwa ne a lokacin da ake ganin akwai yiwuwar Gwamna Nasir El-Rufai yana kokarin rarraba masarautar Zazzau zuwa gida uku domin dukkan manyan masu neman zama sarki su samu sarauta.
Masarautar Zazzau ita ce mafi girma a jihar Kaduna, ta kunshi kananan hukumomi 11 da suka hada da Zaria, Sabon Gari, Giwa, Kudan, Makarfi, Ikara, Kubau, Soba, Igabi, Kaduna North da Kaduna South.
A makon da ta gabata, Gwamna El-Rufai ya umurci masu zaben sarki na masarautar Zazzau su sake sabon zabe na wadanda ke neman zama sarki bayan rasuwar Alhaji Shehu Idris wadda ya rasu ranar 20 ga watan Satumba.
Ana rade-radin cewa gwamnatin jihar tana aiki kan wani kudiri na yi wa tsarin masarautar garambawul da za ta mika wa majalisar jihar don amincewa da shi a matsayin doka.
Dokar inda ta samu amincewar majalisar za ta bada daman nada Magajin Gari, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Kaduna, Yariman Zazzau, Munnir Ja'afaru kuma a nada shi Sarkin Zazzau sai Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu a nada shi Sarkin Kudan a cewar rade-raden.
Yayin gabatar da kasafin kudi na shekarar 2021, Gwamna Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na aiki kan kudirin yi wa masarautu garambawul da ake sa ran mika wa a majalisar. El-Rufai ya ce, "Za mu gabatar da wasu kudororin doka ga majalisar jihar da za su taimaka wurin inganta ayyukan gwamnati."
Source: Legit.ng
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Kamar Ganduje, Gwamna El-Rufai zai yi wa masarautar Zazzau garambawul "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?