
Kalli Bidiyon: Ɗan zanga-zanga ya saci wayar ma'aikaciyar jinya da ta kula da shi ya ɓoye cikin ɗan kamfai
An kama wani mutum da ake zargin ya saci wayar salular ma'aikaciyar jinyar da ke kula da shi a asibiti - A cikin bidiyon da aka wallafa, ma'aikacin asibitin ya yi iƙirarin cewa an yi wa matashin magani kyauta amma ya sace wayar ya saka cikin ɗan kamfansa
Ma'aikacin asibitin ya ce har kuɗin motar da za ta kai mutumin gida an biya masa kyauta amma ya saka musu da sharri Ana zargin wani mutum da aka garzaya da shi wani asibiti mai zaman kansa rai a hannun Allah a ranar 20 ga watan Oktoba da sata.
Ana kyautata zaton yana daga cikin matasan da suka jikkata ne yayin zanga zangar EndSARS da aka yi a Legas. An kai mutumin wani asibitin kudi don masa magani kuma ya kwashe kwanaki ana masa magani kyauta a Asibitin.
A cikin bidiyon da aka wallafa, wani ma'aikacin asibitin ya yi zargin cewa mutumin ya sace wayar salular ɗaya daga cikin ma'aikatar jinyar da ke kula da shi. A cewarsa, mutumin ya ɓoye wayar salular a cikin ɗan kamfansa.
Ga dai bidiyon a ƙasa.
Source: Legit.ng
0 Response to "Kalli Bidiyon: Ɗan zanga-zanga ya saci wayar ma'aikaciyar jinya da ta kula da shi ya ɓoye cikin ɗan kamfai"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?