--
Kalli Bidiyon Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu

Kalli Bidiyon Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu


Wata mota ta cinna kai cikin Masallacin Ka'aba yayinda ta kwaso gudu - Lamarin ya afku ne a ranar Juma'a, 30 ga watan Oktoba, da karfe 10:30 na dare 


Sai dai jami'an tsaro sun yi nasarar damke direban wanda baya a cikin hayyacinsa Rahotanni sun kawo cewa wata mota ta sanya kai gadan-gadan cikin Masallacin Ka’aba a guje, har ta kai ga gab da kofar shiga cikin masallacin taa 89. 


Kakakin gwamnan Makka, Sultan al-Dosari, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Juma’a, 30 ga watan Oktoba, kamfanin dillancin labaran Saudiyya (SPA) ya ruwaito. An tattaro cewa motar ta kustsa kai cikin farfajiar Sarki Fahd, wanda aka hade da masallacin ta baya.


Wani bidiyo da aka wallafa a shafukan zumunta ya nuna yadda motar ta yi awon gaba da ababen kariya sannan ta dangana ga kofar shiga masallacin. 




 Kamar yadda sashin Hausa na BBC ya ruwaito , majiyoyi da dama sun jaddada cewa motar ta shiga farfajiyar masallacin ne ta kan Titi na 15, wanda ita ce babbar hanyar da ta dangane da cikin Farfajiyar Sarki Fahd da ke Masallacin Harami. 


An kuma tattaro cewa babu ko mutum guda da ya jikkata a hatsarin yayinda aka damke direban a nan take. An kuma daure hanayyensa kafin aka tisa keyarsa.


 "Motar ta dangana ga kofar ne yayin da ta kwaso mugun gudu a kan daya da cikin titunan da ke kusa da farfajiyar masallacin ta bangaren kudu. Amma kuma babu wanda ya jikkata," in ji Sultan al-Dosari. Ya ci gaba da fadin cewa: "An cafke direban. Dan Saudiyya ne kuma ba ya cikin hankalinsa. An mika shi wurin masu shigar da kara." 


Shingen da ake sakawa a bakin kofar masallacin ba masu kwari ba ne, abin da ya sa motar ta wancakalar da su kenan, kamar yadda ake iya gani a bidiyon. Shafin Haramain Sharifain ya ce nisan da ke tsakanin ƙofar da motar ta shiga zuwa cikin masallacin bai fi mita 230 ba. 


SOURCE: LEGIT.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Kalli Bidiyon Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?