Yadda uwargida ta hargitsa taron bikin mijinta da wata budurwa
Bidiyon wata mata da ta hargitsa wani aure ya karade shafin sada zumuntar zamani na Instagram - An ga inda wata mata goye da jariri a bayanta ta bayyana a wurin daurin aure, inda ta fallasa sirrin angon
Matar tayi ikirarin cewa Angon mijinta ne, kuma yanzu haka suna da yara kuma suna zaune lafiya da juna Mediagist sun wallafa wani bidiyo a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram, wanda yake nuna wata mata da ta hargitsa wani aure, inda tayi ikirarin cewa ita matar angon ce.
Ranar farin cikin wata Amarya ta koma ranar da tafi kowacce rana bakin ciki da takaici a rayuwarta. An ga wata mata ta bayyana ta fallasa boyayyen sirrin Angon, inda tayi ikirarin cewa mijinta ne shi har suna da 'ya'ya biyu.
Matar ta bayyana a wurin daurin auren da yaro goye a bayanta. Tace lallai har yanzu akwai igiyar aurensa a kanta, kuma suna nan tare cikin soyayya. Ta kara da cewa, bata ga dalilin da zai sa ya kara aure ba, tunda yanzu haka suna da yara tare har biyu.
Source: Legit
0 Response to "Yadda uwargida ta hargitsa taron bikin mijinta da wata budurwa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?