--
 (Kalli Bidiyon)  Mazauna Kwara suma sun kwashi kayan tallafin korona daga wurin ajiya

(Kalli Bidiyon) Mazauna Kwara suma sun kwashi kayan tallafin korona daga wurin ajiya


Mutane a jihar Kwara sun tafi dakin ajiyar kaya sun kwashi kayan abincin tallafin korona - Bidiyon ya nuna mutane maza da mata suna ta gaggawar shiga dakin ajiyar kayan abinci 


An kuma hasko wasu daga cikinsu suna fitowa da kayan abinci a hannunsu da buhunna a kansu Wasu mutane a jihar Kwara sun afka dakin ajiya kayayyaki da ke layin Airport road a Ilorin inda aka ajiye kayan abinci na tallafin annobar korona inda suke ta diban abinda suke so. 


Mutanen da suka hada da maza da mata suna ta tururuwa zuwa wurin da kayan abincin suke suna diba a cikin motocci, babura da wasu ababen hawan.


Wannan na zuwa ne 'yan awanni bayan da wasu mutanen a jihar Osun suka yi kutse a wani dakin ajiye kaya a Ede suna kwashi kayan abincin zuwa gidajensu. 





 Source: Legit

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to " (Kalli Bidiyon) Mazauna Kwara suma sun kwashi kayan tallafin korona daga wurin ajiya"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?