Kalli Bidiyon jarumin da ya sha dambe da masu garkuwa da mutane, ya hana su satar jama'a da tsakar rana
Wani bidiyo mai matukar firgici ya karade kafafen sada zumuntar zamani inda ake kokarin yin garkuwa da mutane da tsakar rana - Amma kuma, wani jarumin maza da ke inda abun ke faruwa ya gaggauta daukar matakin hana garkuwar da mutane
Bidiyon ya karade kafafen sada zumuntar zamani kuma mazauna kasar Afrika ta kudu sun dinga cece-kuce Jama'a da yawa kan zauna su zuba ido ko kuma su nemi wurin boyewa matukar ana aikata laifi saboda tsoron kada ya shafesu. Duk da bai wa kai kariya ba abu ne mara kyau ba, kawai yana nuna yadda jama'a ke mutunta rayuwarsu ne da gudun ta subuce musu.
Amma kuma, akwai jama'a da suka kasance jarumai wadanda saboda kokarinsu basu iya zuba ido su ga ana cutar da wasu. Wani bidiyo mai matukar firgitarwa ya fada kafafen sada zumuntar zamani inda 'yan daba ke kokarin garkuwa da wata yarinya da rana tsaka yayin da take cin abinci da mahaifiyarta. Amma kuma cike da sa'a, wani mutum ya bayyana a take sannan ya dauka mataki.
Ya hana masu garkuwa da mutanen daukar yarinyar. Kamar yadda Yusuf Abramjee ya bayyana, lamarin ya faru a wani wuri ne da ake kira da Bella Napoli, Goldman Crossin, Florida, West Rand. Jarumtar bawan Allah ya sa har jami'an tsaro sun iso sannan suka cafke mmasu garkuwa da mutanen.
A kidnapping attempt in Northcliff. Be vigilant people! pic.twitter.com/4TGOLR1hjC
— Gavin Carter (@GavinCarter83) September 11, 2020
Source: Legit.ng
0 Response to "Kalli Bidiyon jarumin da ya sha dambe da masu garkuwa da mutane, ya hana su satar jama'a da tsakar rana "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?