Kalli Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta
Bidiyon Amaryar da ta tsere a ranar aurenta, ya karade kafafen sada zumuntar zamani - Amaryar ta tsere ne bayan ansa wayar da tayi lokacin da take hanyar zuwa daurin auren nata
Kwatsam sai aka sanar da ita cewa saurayin da zata aura yana lalata da kawar ta Wani bidiyon amaryar da ta tsere ranar aurenta bayan ta gano saurayin da zata aura yana tarayya da kawarta ya karade kafafen sada zumunta. Al'amarin ya faru ne a Area 2, a Garki jihar Abuja.
Kamar yadda aka wallafa a shafin sada zumunta, wata mata na cikin mota zata nufi wurin daurin aurenta, kwatsam sai aka kirata a waya.
Inda aka sanar da ita cewa saurayin da zata aura yana lalata da kawarta ana saura kwanaki kadan a daura aurensu. Take anan amaryar ta dakatar da motar, ta tsere.
Bidiyon ya bayyana yadda kawayenta suka biyo bayanta don gudun kada taje ta salwantar da rayuwar ta. Amaryar tayi ta kuka tamkar zata kashe kanta, inda kawayenta keta kokarin rarrashin ta.
Source: Legit.ng
0 Response to "Kalli Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?