--
KAI TSAYE: Yadda zaben jihar Ondo yake gudana

KAI TSAYE: Yadda zaben jihar Ondo yake gudana


A yau Asabar, 10 ga watan Oktoban 2020, jama'ar jihar Ondo za su kada kuri'unsu domin zaben gwamna na 7 a cikin shekaru 44 da kafuwar jihar. 


Legit.ng za ta dinga kawo muku rahoto dalla-dalla kai tsaye daga jihar Ondo. A zaben yau, jam'iyyyun siyasa 17 wadanda suka hada da APC da PDP duk sun fitar da 'yan takararsu. Masu ruwa da tsaki a jihar sun bayyana tsoronsu na yuwuwar rikici, ganin cewa akwai tarihin rikicin zabe da tashin-tashina a jihar. 


Ma'aikatan zabe sun fara lika rijistar wadanda za su yi zabe Ma'aikatan zabe sun fara isa rumfunan zabe inda suke lika rijistar wadanda za su yi zabe. 



Ma'aikacin wucin-gadi yana wayar wa da masu kada kuri'a kai A Agba, akwati na 08, gunduma ta 4 da ke karamar hukumar Akoko ta kudu masu yamma, shugaban akwatin zaben yana wayar wa masu kada kuri'a kai kafin fara zaben.


Ruwan sama ya tarwatsa masu kada kuri'a a karamar hukumar Akure ta arewa Akwati na 7 a gunduma ta 2 ta karamar hukumar Akure ta arewa, jama'a sun fara kada kuri'a amma ruwa ya tarwatsasu inda suka bazama neman mafaka. 



Dan takarar PDP, Jegede tare da matarsa sun isa rumfar zabensu Dan takarar gwamnan jihar Edo, karkashin jam'iyyar PDP, Eyitayo Jegede, ya isa rumfar zabensa mai lamba 9 a gunduma ta 2 da ke karamar hukumar Akure ta Kudu. 


Jami'an tsaro a kan babura za su kai kayayyakin zabe rumfar zabe a Akure-Owo road a jihar Ondo



Gwamnan Akeredolu ya isa rumfar zabensa da ke Ijebu Owo tare da matarsa Gwamnan jihar Ondo, kuma dan takara a karkashin jam'iyyar APC, Akeredolu Rotimi, ya isa rumfar zabensa tare da matarsa a Ijebu Owo. 



Gwamna Rotimi Akeredolu ya kada kuri'ansa 




Dan majalisa Olubunmi ya isa rumfar zabensa da ke Akoko Olubunmi Tunji-Ojo, shugaban kwamitin majalisar wakilai na NDDC, ya isa rumfar zabensa ta 13,, gunduma ta 3 da ke karamar hukumar Akoko ta arewa maso yamma a jihar. 



Wasu wakilan jam'iyyun siyasa sun fara sayan kuri'a a garin Illaje na jihar Ondo Wasu wakilan jam'iyyun siyasa sun fara sayan kuri'a a garin Illaje @CDDWestAfrica ce ta gano siyan kuri'un @MatthewTPage ya ce irin wannan lamarin ya saba faruwa a garuruwan da ke da wuyan zuwa 



Tsirarun masu zabe sun fara kada kuri'a bayan ruwan sama ya tsagaita a Ondo Masu zabe sun fara dawowa don cigaba da kara kuri'unsu bayan ruwan sama ya tsagaita a Ondo. 



Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "KAI TSAYE: Yadda zaben jihar Ondo yake gudana "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?