--
Duba Jama'a sun saki baki wurin kallon akuyar da ke yawo da kafafu biyu

Duba Jama'a sun saki baki wurin kallon akuyar da ke yawo da kafafu biyu


Wata akuya tayi tafiyar kusan mita 10 da kafafunta 2 kamar yadda mutane ke yi a kauyen Telwera, Bihar a kasar India - Akuyar bata dogara da komai ba, face dage kafafunta 2 na gaba sama tana tafiya jama'a na kallonta suna yi mata bidiyo 


Al'amarin ya sa mutane daga kasashe daban-daban na duniya na son zuwa kauyen don ganin yadda akuyar ke tafiyar Wata akuya a kasar India ta shayar da 'yan Kauyen Telwer, Bihar, mamaki, bayan ta dage kafafunta na gaba sama, tayi tafiya da kafafunta 2 na baya na tsawon sawu 33. 


Bidiyon akuyar mai tafiya da kafafunta 2 yayi ta yaduwa a kafafen sada zumuntar zamani, inda kowa yayi ta al'ajabi. Yayin da akuyar ke tafiyar, mutane da dama sun tsaya suna kallon wannan abin al'ajabi. 


Kamar yadda jaridar New York Post ta ruwaito, masu akuyar sun dade suna koya mata tafiya da kafafu 2 kafin ta fito fili tayi. Kamar yadda bidiyon ya bayyana, akuyar tayi tafiya tamkar mutum na kusan mita 10 a gaban mutane ba tare da ta dogara da komai da sauran kafafun nata na gaba ba. 


'Yan kauyen sun koya mata tafiyar na tsawon awanni kafin ta bayyana gaban jama'a. Al'amarin mai cike da ban al'ajabi yasa mutane daga kasashe da dama sha'awar zuwa kauyen da akuyar take, don ganin akuya mai tafiya da kafafunta 2. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Duba Jama'a sun saki baki wurin kallon akuyar da ke yawo da kafafu biyu "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?