
Hukumar Hisbah da KAROTA za su fara kama masu batsa wurin siyar da magungunan gargajiya
Gwamnatin jihar Kano za ta fara kama masu magagungunan gargajiya da ke amfani da kalaman batsa don tallata hajojinsu - Sakataren ma'aikatar lafiyar jihar, Dr Usman Tijjani Aliyu, ya sanarwa manema labarai a ranar Laraba, inda yace yanzu haka an samar da wani kwamiti
Ya ce kwamitin zai hada da ma'aikatar lafiya, jami'an KAROTA da na Hisbah za su dinga kama masu magungunan gargajiyar Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta fara kama masu magaungunan gargajiya da suke amfani da kalamen batsa wurin tallar magungunansu, Daily Trust ta ruwaito.
Gwamnatin ta kirkiri wani kwamiti da ke karkashin kwamishinan lafiya, Dr Ibrahim Tsanyawa, KAROTA, Hisbah da sauran jami'an tsaro a matsayin 'yan kwamitin. Sakataren ma'aikatar lafiyar jihar, Dr Usman Tijjani Aliyu, ya shaida wa manema labarai hakan a ranar Laraba, inda yace an gama duk wasu shirye-shirye don fara ayyuka a kwamitin.
Ya ce jami'an Hisbah da na KAROTA ne za su dinga kama masu magungunan gargajiyar su gabatar da su kotu. Ya kara da cewa, suna tsananta amfani da kalaman batsa wurin tallata hajojinsu wanda gwamnati ba za ta lamunci hakan ba.
Source: Legit.ng
0 Response to "Hukumar Hisbah da KAROTA za su fara kama masu batsa wurin siyar da magungunan gargajiya"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?