
Hotunan gine-gine 10 mafi darajar kudi a fadin duniya, Ka'aba ne na 1
Gine-gine sun da matukar daukar hankalin jama'a a fadin duniya - MSN ta yi bincike a kan gine-gine 30 mafi darajar kudi a fadin duniya
Ana ganin cewa har nan gaba ba za a samu gini mafi tsada kamar Ka'aba ba MSN Money kungiya ce da ke kula da hada-hadar kudi, hannayen jari, kadarori da kuma lamuni a duniya.
Ta yi bincike a kan gini 30 mafi tsada da darajar kudi a fadin duniya kuma kasar Saudiya ce a kan gaba da gine-gine biyu. Ga dai jerin gini 10 mafi darajar kudi a duniya tare da hotunansu.
1. Masallacin Ka'aba, Makkah: Dala biliyan 100
Darajarsa ta kai dala biliyan 100. Masu kiyasi suna ganin akwai matukar wahala a samu ginin da zai wuce shi a daraja a fadin duniya koda kuwa nan gaba.
2. Ginin Abraj Al Bait, Makkah: Dala biliyan 16
Wannan ginin an kammala shi a 2012 kuma an yi shi ne domin mahajjata musamman shugabannin duniya da masu hannu da shuni.
Baya ga tsananin tsadarsa, yana da fuskar agogo mafi girma a duniya. Wannan ginin yana nan a garin Makkah da ke kasar Saudi Arabia.
3. Wurin shaƙatawa Marina Bay Sands, Singapore: Dala biliyan 6.2
Wurin shakatawa na Marina Bay Sands da ke Singapore ya kasance katafaren wuri mai dakunan alfarma. An kammala gininsa a 2010 kuma tabbas a halin yanzu darajarsa ta karu.
4. Hedikwatar kamfanin Apple, Cupertino: Dala biliyan biyar
Gini ne wanda aka fara a 1984. A halin yanzu darajarsa ta kai jimillar kuɗi dala biliyan 3.9. Ginin yana nan ƙasar Romaniya.
Wannan wuri yana daya daga cikin manyan otal na duniya. yana da rukunin dakuna da wurin caca. An kaddamar da shi a 2005 a Wyn. Yana da dakuna 2,1716
An yi ginin a 1984 a kan kudi dala biliyan 1.4. Fadar ita ce masarauta mafi girma a duniya. Tana da yawan dakuna 1,788 da manyan dakunan taro 5,000.
Source:Legit.ng
0 Response to "Hotunan gine-gine 10 mafi darajar kudi a fadin duniya, Ka'aba ne na 1 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?