
Hotuna: Ango ya garzaya wurin zanga-zangar EndSars daga wurin ɗaurin aurensa
Wani ango a Najeriya ya tafi wurin zanga-zangar EndSars a ranar da aka ɗaura masa aure ko kaya bai canja ba
Angon ya wallafa hotunan sa sanye da kayan da aka ɗaura masa aure ɗauke da takarda da cewa 'ku rushe rundunar SARs yanzu'
Matasa da dama a jihohi daban-daban a Najeriya sun kwashe kwanaki suna zanga-zangar neman ganin an rushe SARs tare da yin wasu sauye-sauye a rundunar ƴan sanda
Wani ɗan Najeriya ya shiga ya zanga-zangar da matasa suka yi a kasar na neman rushe rundunar ƴan sanda ta musamman na SARs a ranar da aka ɗaura masa aure a Legas.
An ɗauki hotunan mutumin mai suna @OgebeniKunle1 a Twitter sanye da kayan da ya tafi wurin ɗaurin aure da su a jikinsa yana rike da takarda ta zanga-zanga.
Hakan na nuna akwai alamun bayan ɗaurin auren bai wuce ko ina ba sai wurin zanga-zangar domin shima ya bada tasa irin gudummawar. A hotunan da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya rubuta cewa:
"A yau na shiga zanga-zangar #EndSARS bayan an ɗaura min aure a kotu. Kada SARS su kashe wa matata mijin ta."
A wani labarin daban, mutum tara ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Zubairu Mato, Kwamandan Hukumar Kiyayye Hadurra ta Kasa, FRSC, a jihar cikin wata sanarwa da ya ce hatsarin ya faru ne misalin karfe 9 na safe da ya ritsa da mota da adaidaita sahu a hanyar Kano zuwa Zaria a kauyen Imawa da ke karamar hukumar Kura.
Source: Legit
0 Response to "Hotuna: Ango ya garzaya wurin zanga-zangar EndSars daga wurin ɗaurin aurensa"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?