
Hilary Clinton Ta Gargadi Buhari A Kan Kashe Masu Zanga-Zangar #EndSARS
Wednesday, 21 October 2020
Comment
Tsohuwar Sakatariyar Gwamnatin Amurka, Hilary Clinton ta ta kirayi shugaban kasa Muhammadu Buhari da rundunar sojin kasa na Najeriya da su daina zub da jinin masu zanga-zangar lumana ta kin jinin rundunar tsaro ta SARS.
Misis Clinton ta yi wannan kira ne cikin wani dan taikataccen sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Talata, inda ta Ambato Shugaba Buhari da Rundunar Sojin Kasan Najeriya da su daina kasha matasan da ke zanga-zangar lumana.
Clinton wadda tsohuwar Sanata ce kuma ta nemi takarar shugabancin kasar Amurka har karo uku, ta ce “Ina kiran Muhammadu Buhari da sojojin kasan Najeriya, dasu daina kasashe matasa masu zanga-zangar #EndSARS.”
A Talatar da ta gabata ce aka yi fargabar mutane da dama sun mutu bayan sojoji sun bude wa masu zanga-zangar EndSARS wuta a dandalin Lekki da ke birnin Legas.
Kawo yanzu, tuni dai zanga-zangar ta rikide zuwa rikici tsakanin masu gudanar da ita da wasu da ake zargi ’yan daba ne a wasu manyan biranen kasar da suka hada da Kano, Benin da Abuja.
Source: Aminya Daily Trust
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:
LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:
KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN:
KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK:
@TWITTER:
KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765
0 Response to "Hilary Clinton Ta Gargadi Buhari A Kan Kashe Masu Zanga-Zangar #EndSARS"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?