
Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure
Wata daya bayan daurin aure, Hana da maigidan sun saki sabbin hotuna - An daura musu aure a Masallacin fadar shugaban kasa ta Aso Villa A daurin aurensu, wanda manyan mutane a fadin Najeriya suka halarta, Amaryar da Angon sun samu albarkan iyaye da manyan malamai.
Amma an yi cece-kuce kan yadda aka gudanar da daurin auren. Yan Najeriya da dama sun caccaki iyalan shugaban kasa a kan karya dokar babban bankin Najeriya (CBN) a wajen bikin Hanan Buhari, daya daga cikin yaran shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Mutane da dama sun kuma yi wasti da take dokar bayar da tazara a tsakanin jama’a wanda hukumar yaki da yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayar don hana yaduwar cutar Coronavirus.
Bikin ya samu manyan jami’an gwamnati da yan siyasa. Hotuna da bidiyon bikin ciki harda wanda uwargidar shugaban kasar, Aisha Buhari ta wallafa a shafinta na Instagram sun yi fice a karshen makon.
Turan 'da ne ga Mahmud Sani Sha'aban, tsohon dan majalisa wanda ya wakilci mazabar Zaria a majalisar wakilan tarayya daga Mayun 2003 zuwa 2007. Hakazalika ya yi takaran kujeran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN).
Kalli hotunan:
Source: Legit.ng
0 Response to "Hanan Buhari da Mijinta Muhammad Turad sun saki hotunansu na farko bayan aure "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?