--
Gwamna ya fatattaki hadimansa na musamman a kan tsaro saboda kona ofisoshin 'yan sanda

Gwamna ya fatattaki hadimansa na musamman a kan tsaro saboda kona ofisoshin 'yan sanda


Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya kori hadimansa na musamman da ke fannin tsaro - Ya hada da wasu manyan jami'ansa uku sakamakon kone ofisoshin 'yan sanda da aka yi - Gwamnan ya ce ya yi hakan ne 


saboda rashin kwarewarsu a fannin tsaron da ya saka su Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori hadimansa na musamman da ke bashi shawara a kan tsaro da wasu jami'ai uku a kan kone ofisoshin 'yan sanda da wasu kadarorin gwamnati a jihar. 


A wata takardar da ta fito daga sakataren gwamnatin, Kenneth Ugbala, a ranar Lahadi, ya ce mai bada shawara na musamman a fannin yada labarai, Nchekwube Aniakor da wasu shugabanni uku, ya sallamesu. Shugabannin da aka sallama sun hada da Amos Ogbonnaya, Jerry Okorie Ude da Martha Nwankwo. 


A wuraren ne 'yan daba suka kai wa ofisoshin 'yan sanda hari a Abakaliki, babban birnin jihar a ranar Laraba. Bata-garin sun tarwatsa wasu kayayyakin gwamnati ballantana na kan tituna a sassa daban-daban na jihar. Ugbala ya ce gwamnan a kokarinsa na ganin tsaro ya tabbatar a jihar ne ya kori hadimansa, Premium times ta wallafa. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Gwamna ya fatattaki hadimansa na musamman a kan tsaro saboda kona ofisoshin 'yan sanda "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?