--
Ganduje ya dakatar da hadiminsa Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Buhari

Ganduje ya dakatar da hadiminsa Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Buhari


Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da mashawarcinsa na musamman kan watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai 


Ganduje ya dakatar da kakakinsa ne bayan ya soki Shugaba Muhammadu Buhari game da zanga-zangan neman soke 'yan sandan SARS da al'umma suka yi 


Yakasai ya nuna takaicinsa kan abinda ya kira rashin tausayi da halin ko-in-kula da Shugaba Buhari ke nuna wa 'yan Najeriya 


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya dakatar da mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai game da wasu 'maganganu masu kaushi da ya yi kan Shugaba Muhammadu Buhari a dandalin sada zumunta.' 


Kwamishinan watsa labarai na Kano, Muhammad Garba da ya bada sanarwar yau Lahadi da rana ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take. 


Ya ce duk da cewa hadimin gwamnan yana da ikon yin tsokaci kan batutuwa don ra'ayinsa, a matsayinsa na mutum mai rike da mukami, yana da wahalar a banbance ra'ayinsa da matsayin gwamnan a kan batutuwa da suka shafi al'umma.


Gwamnan ya gargadi masu rike da mukaman siyasa da ma'aikatan gwamnati su kiyayye yin maganganu da ka iya tada zaune tsaye da janyo cece-kuce. Tunda farko Yakasai ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: 


"Ban taba ganin gwamnati mara tausayi ba kamar irin ta Buhari. Lokuta da yawa mutane suna shiga mawuyacin hali kuma suna bukatar ya basu kwarin gwiwa cewa yana daukan matakai a kai amma baya yin hakan. Halin ko-in-kula da ya ke dashi na daban ne."


A wani rubutun da ya wallafa a Twitter: "Yi wa al'ummar ka magana kan abubuwan da ke damunsu ya zama tamkar alfarma ka ke musu. Ka gaza ware ko da minti biyar ka kwantar wa mutane hankali, mutanen da ka bi jihohi 36 ka nemi kuri'arsu, abin takaici ne wannan." 


Source: Legit 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Ganduje ya dakatar da hadiminsa Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Buhari "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?