Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi ga masu ikirarin Najeriya za ta tarwatse
Gwamnatin tarayya tayi ala-wadai da 'yan Najeriyan dake miyagun maganganu akan tarwatsewar kasa - Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya ce wadannan kalamai na nuna rashin kishin kasa -
Shehu yace a yanzu haka Shugaba Buhari ya tsaye tsayin-daka wurin ganin ya ceto Najeriya daga dukkanin baraka Gwamnatin tarayya tayi ala-wadai akan 'yan Najeriyan dake cewa Najeriya na gab da tarwatsewa.
Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya fadi hakanne a wata takarda ta ranar Lahadi, 14 ga watan Oktoba wanda yake cewa rashin kishin kasa ne furta wadannan kalamai. Gwamnatin tarayya ta zargi wasu 'yan Najeriya akan maganganun nuna rashin kishin kasa. Garba Shehu ya ce gwamnatin Buhari ba za ta lamunci irin wadannan kalubalan ba.
Gwamnati zata tsaya tsayin-daka wurin kawar da duk wani abu da zai tada tarzoma da kuma hankulan 'yan kasa. Ya ce gwamnati zata dage wurin kawar da matsalolin rashin tsaro da kuma cutar COVID-19.
Mai magana da yawun shugaban kasan, yace gwamnatin tarayya ba za ta dauki wani matakin da zai cutar da 'yan Najeriya miliyan 200 ba, wanda hakan ne abu na farko da Shugaban kasa ya dace yayi. Shehu ya kara da cewa, "Buhari zai cigaba da dagewa wurin ganin ya kawo karshen duk wani kalubale dake damun Najeriya."
Source: Legit.ng
0 Response to "Fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi ga masu ikirarin Najeriya za ta tarwatse "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?