EndSars: Masu zanga-zanga sun kashe dan sanda, sun raunata wani sun kuma sace AK47
IGP na 'yan sandan Najeriya ya yi tir da kisar da wasu masu zanga-zanga suka yi wa jami'in dan sanda a jihar Delta - IG Adamu ya yi gargadin cewa rundunar 'yan sanda ba za ta amince wasu da ke ikirarin zanga-zanga su sake kashe wani jami'in tsaro ba
Shugaban 'yan sandan ya ce al'umma na da ikon yin zanga-zangan lumana amma dole ayi shi bisa yadda doka ta tanada Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya yi Allah wadai da harin da masu zanga-zangar #ENDSARS suka kai wa 'yan sanda a Ughelli jihar Delta a ranar 8 ga watan Oktoba.
Matasa a Ughelli sun fito kwansu da kwarkwata sun yi zanga-zanga na neman a soke rundunar 'yan sanda ta musamman masu yaki da 'yan fashi wato SARS.
Sanarwar da kakakin 'yan sandan Najeriya, DCP Frank Mba ya fitar ya ce masu zanga-zangar sun kashe wani Kofur Etaga Stanley a Ugelli kuma sun raunta wani jami'in, Saja Patrick Okuone.
"Masu zanga-zangar sunyi awon gaba da AK 47 guda daya mai lamba 56-2609008 da harsasai 25 da ke tare da marigayin a lokacin da abin ya faru,"
a cewar sanarwar Mba. Sufetan 'yan sandan da ya bayyana harin a matsayin zalunci ya yi gargadin cewa rundunar ba za ta lamunci hari a kan jami'anta ba ko wani jami'in tsaro daga wasu da ke ikirarin yin zanga-zanga.
IGP din ya ce 'yan kasa na da damar yin zanga-zanga na lumana amma ya zama dole ayi shi cikin tsari da kiyaye dokokin kasa.
The Inspector General of Police, IGP M.A Adamu, NPM, mni has condemned the unprovoked and violent attack on policemen and damage to police operational vehicles and other assets by ENDSARS protesters in Ughelli, Delta State, on Thursday, 8th October, 2020.
— Nigeria Police Force (@PoliceNG) October 9, 2020
Sergeant Patrick Okuone with serious body injury sustained from gunshot by the protesters. The protesters also carted away one (1) service AK47 rifle with breach no 56-2609008 and 25 rounds of live ammunition that was with the deceased at the time of the incident.
— Nigeria Police Force (@PoliceNG) October 9, 2020
The IGP notes that protest by citizens remain a legitimate means for airing their concerns and views. It must however be carried out with all sense of responsibility and within the confines of the law.
— Nigeria Police Force (@PoliceNG) October 9, 2020
Source: Legit.ng
0 Response to "EndSars: Masu zanga-zanga sun kashe dan sanda, sun raunata wani sun kuma sace AK47 "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?