
ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje
Fatima Ganduje-Ajimobi, 'yar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ta tofa albarkacin bakinta kan zanga-zangar da matasa ke yi a Najeriya game da 'yan sanda
Matasan sun kwashe kwanaki sun fita zanga-zanga kan tituna suna neman soke rundunar 'yan sanda ta musamman na SARS da wasu bukatu
Fatima Ganduje ta shawarci matasa su tanadi katin zabe, su kada kuri'unsu kuma su tabbatar an kirga kuri'un don kawo irin sauyin da suke so a kasar
Ƴar gidan gwamnan Kano, Fatima Ganduje-Ajimobi ta magantu a kan zanga-zangar #ENDSARS da ake don nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda
A wani rubutu data wallafa a shafinta na Instagram ranar Asabar, 17 ga Oktoba, tayi kira ga mutane su mallaki katin zaben su sannan kuma bayan ya kaɗa kuri'arsa ya tabbatar an kirga kuri'ar tasa.
"Kuyi zabe kuma kada ku bar mazabar har sai an ƙirga kuri'arku. Kuyi gangami ku raka kuri'unku," Fatima ta rubuta. "Ku tsaya kai da fata a wajen tattara sakamako sannan ku tabbatar an ƙirga kuri'arku. Matasa sune mafiya rinjaye kuma su za su ceto kasar mu Najeriya.
(#ENDSARS #ENDOPRESSION #FGA)," ta sake rubutawa. Anasa bangaren, mijinta Idris Ajimobi ya yi kira ga matasa da su tabbatar sun tanadi katin zabensu don tunkarar babban zaben 2023.
Source:Legit.ng
0 Response to "ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?