
EndSARS: Abubuwa 10 da Buhari ya yi magana a kai a jawabin jiya da ya yi
A jiya da yamma Shugaban kasa ya fito ya yi wa al’ummar Najeriya jawabi - Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi a dakatar da zanga-zangar haka na
Gwamnati ta yi alkawarin kare ran al’umma da kara albashin jami’an tsaro A ranar Alhamis, shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan kasa jawabi a karon farko bayan zanga-zangar #EndSARS ya fara daukar wani sabon salo.
Jaridar Daily Trust ta tattaro manyan kanun da ke cikin jawabin da shugaban kasar ya yi a jiya. Mun tsakuro wasu daga cikinsu:
1.Akwai masu wata manufa Shugaban kasar ya yi gargadi cewa akwai wasu bata-gari da su ka shige cikin rigar #EndSARS domin su kawo tarzoma. Ya kuma fada wa sauran kasashe su yi bincike, kafin su tsoma-baki.
2. Danyen aikin SARS Muhammadu Buhari ya yarda cewa da gaske dakarun SARS su na cin zarafin al’ummar Najeriya.
3. Damar zanga-zanga Shugaban Najeriyar ya ce duk wani ‘dan kasa ya na da damar fita zanga-zanga, amma bai da ikon ya shiga hakkin sauran jama’a.
4. Bukatun #EndSARS Buhari ya ji kukan masu zanga-zangar #EndSARS, ya ce don haka aka ruguza sashen, sannan aka kama hanyar biyan sauran bukatun.
5. Duka wa wada ba gajiya wa A jawabin shugaban kasar, ya ce gaggawar dakatar da aikin SARS da aka yi, ya sa wasu a Najeriya su na yi wa gwamnati kalon rauni.
6. Abin takaici Babu dalilin barna da ta’adin da wasu tsageru su ka rika yi da sunan #EndSARS inji shugaban kasar.
7. Sabon tsarin albashin jami’an tsaro Gwamnatin tarayya ta bada umarnin ayi maza a shigo da sabon tsarin albashin jami’an tsaro.
8. Kokarin gwamnatin APC Babu gwamnatin da ta yi kokarin yaki da talauci a tarihin Najeriya irin ta mu inji Buhari.
9. Ya isa haka nan Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasa su canza salo, su daina zanga-zanga domin ya ji kukansu.
10. A koma bakin-aiki Daga cikin abin Buhari ya fada wa ‘Yan kasa shi ne a koma bakin-aiki, sannan jami’an tsaro su kare rayuka. Dama tun a jiya da rana, kun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari zai dauki muhimmin mataki game da matsalar tsaro.
Janar Babagana Monguno ya bayyana wannan. Ya yi wa ‘Yan Najeriya albishir kafin shugaban kasa ya yi bayani kan zanga-zangar #EndSARS.
I must warn those who have hijacked and misdirected the initial, genuine and well-intended protest of some of our youths in parts of the country, against the excesses of some members of the now disbanded Special Anti-Robbery Squad (SARS).
— Muhammadu Buhari (@MBuhari) October 22, 2020
Source: Legit
0 Response to "EndSARS: Abubuwa 10 da Buhari ya yi magana a kai a jawabin jiya da ya yi "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?