
Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi martani a kan tsine mata a Masallatai
Zangar-zangar lumana domin nuna kyamar rundunar 'yan sanda ta SARS ta rikide zuwa kazamin rikici a sassan Najeriya - 'Yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, na daga cikin jagororin matasan da suka assasa tare da jagorantar zangar-zangar ENDSARS
Sai dai, Aisha ta sha suka da caccaka daga wasu shugabannin siyasa, musammam ma su rike da mukamai, da kuma wasu malamai 'Yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta yi shagube ga Musulman da suka dinga caccakarta saboda 'ta yi uwa, ta yi makarbiya' a zanga-zangar ENDSARS.
Aisha, wacce sunanta ya kara karada gari saboda zanga-zangar ENDSARS, ta ce ko kadan hakan bai taba damunta ba. "Na ji cewa na sha tsinuwa a Masallatai, mutane suna zama domin kawai su tsinemin bayan sun idar da Sallah.
"Tambayata wurinsu guda daya ce; sau nawa suka yi min irin wannan tsinuwar a lokacin da nake caccakar tsohon shugaban kasa Jonathan! Dukkanmu tsinannu a Najeriya," kamar yadda Aisha ta rubuta, tare da hadawa da alamar shekewa da dariya, a shafinta na tuwita.
Heard I am being cursed in mosques! People finish praying and take time out to curse me in their prayers
— Aisha Yesufu (@AishaYesufu) October 30, 2020
I have asked they should please let me know how many of these curses they rained on me when I was making same demands during GEJ!
We are all already cursed in Nigeria 🤣
'Yar gwagwarmayar na daga cikin wadanda suka assasa tare da jagorantar matasan da suka fito domin gudanar da zanga-zangar ENDSARS. Sai dai, zanga-zangar ENDSARS ba ta samu wata karbuwa ba a jihohin arewa, musamman jihohin yankin arewa maso yamma, da Aisha ta fito.
Zakewarta yayin zanga-zangar ya jawo mata shan suka da caccaka a wurin shugabannin siyasa, musammam masu rike da mukamai, da wasu malaman addini.
Zanga-zangar lumana ta neman a rushe rundunar 'yan sanda ta SARS ta rikide zuwa rikici da tarzoma a jihohi da dama. Ganin irin tarzomar da zanga-zangar ta haifar ne yasa Ƙungiyar tuntuba da cigaban Arewa (ACF) ta yi gargaɗin cewa ya kamata shugabannin Najeriya su sani za a iya rasa zaman lafiya a kasa idan har suka cigaba da yin burus da matasa da kuma buƙatunsu.
Source: Legit.ng
0 Response to "Dukkanmu tsinannu ne a Nigeria - Aisha Yesufu ta yi martani a kan tsine mata a Masallatai"
Post a Comment
Tell us what you think about this article?