--
Dilalin bindigu ya mutu yayin da ya yi yunkurin tserewa hukuma a Katsina

Dilalin bindigu ya mutu yayin da ya yi yunkurin tserewa hukuma a Katsina

 Wani da ake zargi mai sayar wa 'yan bindiga makamai ne ya mutu a karamar hukumar Safana a Katsina - Jami'an tsaro sun tsayar da shi a lokacin da suka gan shi a babur zai nufi cikin daji amma sai ya ki tsayawa 


Jami'an tsaron sun harbe shi a kafa yayin da ya ke yunkurin guduwa kuma an gano harsasai a karkashin siddin babur dinsa daga bisani 


Wani mutum mai shekaru 35, Abubakar Haruna da ake zargin mai garkuwa ne kuma mai sayar wa 'yan bindiga makamai ya mutu sakamakon raunin harsashi yayin da ya yi yunkurin tserewa jami'an tsaro a ranar Laraba. 


A cewar 'yan sanda, an harbi Haruna dan asalin kauyen Ilela a karamar hukumar Safana a kafarsa a mahadar Tsaskiya da ke karamar hukumar ta Safana. 


An ce yana dauke da harsashi masu tsawon 7.62mm na bindigar AK 47 guda 600 zai tafi dajin Rugu ya kai wa 'yan bindiga ne 'yan sanda da 'yan banga suka kama shi. Ya boye harsashin cikin wani buhu da ke karkashin siddin babur din da ya ke tukawa. 


Kakakin 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya ce, "An kama bata garin a Tsaskiya junction yana tuka wata babur kirar Bajaj mara rajista zai shiga daji. 


"Wanda ake zargin ya ki tsayawa a lokacin da aka bukaci ya tsaya, hakan yasa aka harbe shi a kafa." An yi holen gawar Haruna a hedkwatan rundunar 'yan sanda na jihar Katsina a yammacin ranar Alhamis. 

Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765


0 Response to "Dilalin bindigu ya mutu yayin da ya yi yunkurin tserewa hukuma a Katsina"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?