--
Dalilin da yasa muka bar jama'a suka kwashe tallafin korona - Dan sanda

Dalilin da yasa muka bar jama'a suka kwashe tallafin korona - Dan sanda


Tunda zanga-zangar EndSARS ta canja salo ta koma sace-sace da kone-konen dukiyoyin gwamnati da na al'umma, 'yan sanda sun zura ido suna kallo - Mutane da dama sun yi ta mamakin yadda jami'an suka zurawa sarautar Allah ido basa daukar wani mataki a kan wannan barakar a jihohi 


Wani jami'in 'yan sanda, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana hujjoji kwarara wadanda suka sa jami'an suka dauki wannan matakin Sace-sace da matasa ke ta yi sun cigaba da faruwa a ma'ajiyar gwamnati, inda suke sace kayan tallafin COVID-19 wadanda ya kamata a raba tun lokacin da gwamnati ta saka kulle. 


Duba da faruwar wannan lamarin ne 'yan sanda suka zura idanu suna kallo ana sata basu daukar wani mataki a kai, Daily Trust. Wani 'Dan sanda da ya bukaci a sakaya sunansa ya yi magana a kan zura idon da 'yan sandan suka yi a kan al'amarin a matsayinsa na jami'in tsaro. 


Kamar yadda aka yi hira da shi, inda aka tambayeshi dalilin zurawa masu zanga-zangar ido suna ta bankawa kayan gwamnati wuta bayan sace wasu. Cewa yayi: "Kun san cewa 'yan ta'adda sun tsani ganin 'yan sanda, kuskuren 'yan sanda na farko shine rushe rundunar SARS, saboda a watannin karshen shekara ba'a rushe kungiya mai yaki da ta'addanci irin SARS.


"Kamata yayi a tabbatar an yi bincike Mai tsanani a kan lamarin, sai ayi kokarin yin gyara a kan barakar da aka samu. "Na biyu, kamata yayi ace a Najeriya ana yin horo mai tsanani ga jami'an 'yan sanda, tun daga kan kwamishina har kasa, domin wasu jami'an ba su san hakkokin jama'a ba balle har su karesu.


"Ta ya za'ayi ace wanda aka hora yayin shiga aikin 'yan sanda tun shekaru 15 zuwa 20 su san sababbin tsarin da kasa ta tanadar a shekarunnan?" 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "Dalilin da yasa muka bar jama'a suka kwashe tallafin korona - Dan sanda "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?