
Dalibi ya fille kan malaminsa saboda ya yi batanci ga manzon Allah a Faransa
Wani malamin makaranta a Faransa ya sheka lahira hannun dalibinsa sakamakon zana hoton isgilanci ga manzon Allah (SAW) - Wannan abu ya faru ne a wajen makaranta dake wani gari mai nisan kilomita 30 da birnin Paris
Malamin ya yi amfani da zanen manzon Allah wajen bayani kan yanci a kasar Faransa Wani dalibin makaranta ya fille kan malaminsa bayan ya yi zanen isgilanci ga Annabi Muhammad a harabar makarantar ranar Juma'a. Matashin ya nuna alfaharinsa na rashin iya jure ganin ana batanci ga manzon Allah yayi shiru.
Har yanzu ba'a bayyana hotonsa ba amma jami'an yan sanda sun bude masa wuta kuma suka kasheshi, a cewar Reuters. Wannan abu ya faru ne misalin karfe 5 na yamma a Conflans Saint-Honorine, wani gari dake kusa da birnin tarayyar Faransa, Paris. Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron, ya yi alhinin abinda ya faru.
An fara samun wannan matsala ne tun lokacin da jaridar Charlie Hebdo ta wallafa hotunan barkwancin da suka yi a 2015 na batanci ga Annabi Muhammadu (SAW). Sakamakon haka wasu mutum biyu masu iƙirarin jihadi suka kai harin bindiga a ofishin mujallar a ranar 7 ga watan Janairun 2015.
Hotunan barkwancin da suka zana akan Annabi Muhammadu, sun zamo abun batanci da cin zarafi, wanda ya sa har kungiyar Said da Cherif Kouachi suka farmaki ginin jaridar. A harin, mutane 12 ne suka rasa rayukansu.
Wadannan hare haren su ne mafarin kai hare haren masu ikirarin jihadi a fadin Faransa. Shafin farko na mujallar na ɗauke da zanen barkwanci har guda 12 na Annabi Muhammad S.A.W, waɗanda aka wallafa a wata jaridar harshen Danish kafin aka wallafa su a mujallar Charlie Hebdo.
Daya daga cikin zanen barkwancin ya nuna Annabi Muhammad S.A.W sanye da bam a kansa a maimakon rawani.
Source: Legit.ng
0 Response to "Dalibi ya fille kan malaminsa saboda ya yi batanci ga manzon Allah a Faransa "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?